Rikicin Keyamo da Sanatoci: Shugaban Majalisa ya soki Ministan Shugaba Buhari
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce karamin ministan kwadago na kasa, Festus Keyamo bai isa ya jawo sabani tsakanin ‘yan majalisa da masu zartarwa ba.
Sanata Ahmad Lawan ya dura kan Festus Keyamo SAN, ya ce shugaban kasa ne kadai wanda ya ke da ikon zartarwa a gwamnatin Najeriya.
Ahmad Lawan ya ce ministan kwadagon bai da tasirin da zai iya kawo matsala tsakanin ‘yan majalisar tarayya da bangaren masu mulki domin su na kan shafi guda da shugaban kasa.
Lawan ya bada amsa ne yayin da aka tambaye sa game da matsayar majalisa a kan Naira biliyan 52 da aka warewa hukumar NDE domin daukar matasa aiki a cikin kasafin kudin 2020.
Shugaban majalisar ya ce har yanzu su na kan bakansu na cewa an dakatar da shirin daukar matasa 774, 000 aiki.
KU KARANTA: Sanatoci sun kori Keyamo daga Majalisa
Ahmad Lawan ya ce sai lokacin da gwamnati ta fito ta yi bayanin yadda za ta dauki hayar wadannan matasa, sannan za su bada damar a cigaba da wannan shiri.
“Bari in fara maida martani ga maganar cewa ba mu tare da masu zartarwa. Bari in fada maku cewa saboda kishin kasa majalisa ta amince da wannan kudi N52b domin a dauki matasa aiki a fadin kasar nan.”
“A lokacin da aka amince da wannan kasafi, majalisa ta na kaffa-kaffa da cewa hukumar NDE ce za a ba alhakin wannan aiki, domin ita ce ta san yadda za a dabbaka tsare-tsaren.” inji Lawan.
A game da takkadamar da aka samu tsakanin Festus Keyamo da sanatoci a gaban kwamiti, Lawan ya ce ‘yan majalisa sun yi daidai domin su na da hurumin su fito su yi tambayoyi.
Lawan ya ce su na nan a kan cewa ba za a cigaba da dabbaka shirin ba sai sun gamsu, kuma hukumar NDE ce za ta zakulo matasan da za a ba wannan aiki na karamin karfi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng