Ray Hushpuppi: Yadda kafar Google ta sa aka yi ram da gawurtaccen ‘dan damfara

Ray Hushpuppi: Yadda kafar Google ta sa aka yi ram da gawurtaccen ‘dan damfara

Jaridar The Cable ta fitar da rahoto cewa akawun dinsa na Google ne ya yi sanadiyyar da aka kama Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi.

An yi fam da Hushpuppi ne a garin Dubai kwanaki, daga nan jami’an kasar Amurka su ka yi nasarar dauke shi daga UAE domin ya amsa laifuffukan da ake tuhumarsa da su.

Ana zargin Hushpuppi a gaban wani kotun Amurka da laifin wawurar dukiyar mutane ta hanyar damfara da zamba cikin aminci.

A wasu takardu da su ka shigo hannun The Cable, an gano cewa jami’an FBI sun yi nasarar gano inda Hushpuppi ya ke ne bayan ya aika sako ta yanar gizo da wata wayarsa ta iPhone.

Ma’aikatan hukumar FBI da ke bincike a Amurka sun gano cewa Hushpuppi ya nemi a turo masa wasu kudi zuwa wani asusunsa.

Da aka yi bincike a game da bayanan da aka samu daga wani shafin Instagram, an gano cewa an yi rajistar akawun din da sunan ‘RAY’ a Dubai.

KU KARANTA: APC ta na alakanta Jagororin PDP da Hushpuppi

Ray Hushpuppi: Yadda kafar Google ta sa aka yi ram da gawurtaccen ‘dan damfara
Ray Hushpuppi
Asali: Instagram

Akwatin email din da aka yi rajistar Instagram din da shi kuwa shi ne rayhushpuppi@gmail.com, da kuma lambar wayar salula +971502818689.

An yi rajistar wannan shafi a dandalin Instagram ne a cikin watan Oktoban 2012. Bincike ya nuna ana amfani da shafin ne daga wani adireshi da ke kasar UAE.

Kamar yadda rahoton ya bayyana mana, FBI ta gano wannan ne bayan ta binciki adireshin IP da ake amfani da shi daga wayoyin salular wannan mutumi da ake zargi.

Rahotannin da aka samu daga kamfanin Snap Inc, ya nuna cewa wani mai amfani da Hushpuppi5 a dandalin Snap Chat ya yi amfani ne da lamba +971565505984 da kuma akwatin rayhushpuppi@gmail.com wajen rajista.

Karyar wannan mutumi mai suna The Billionaire Gucci Master!!! a SnapChat ta kare bayan kamfanin Apple ya bada akawun dinsa na Gmail dauke da tikitin jirginsa da fasfon kasar waje da duk wasu asirisa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel