Babu gaskiya a zargin Mahadi Shehu – inji Sakataren gwamnatin Katsina

Babu gaskiya a zargin Mahadi Shehu – inji Sakataren gwamnatin Katsina

Bayan Alhaji Mahadi Shehu ya fito gaban Duniya ya zargi gwamnatin Katsina da yin facaka da Naira biliyan 24, sakataren gwamnatin jihar ya maida martani a ranar Litinin.

Dr. Mustapha Muhammad Inuwa ya kira taro da ‘yan jarida inda ya yi bayani game da zargin da ake yi wa gwamnatinsu ta APC, a jawabinsa ya bayyana abin da ya ce shi ne gaskiyar lamarin.

Dr. Mustafa inuwa ya bayyana cewa tun a lokacin gwamnatin Ummaru Musa ‘Yar’adua aka bude asusun kudin tsaro a jihar Katsina, ya ce wannan asusu ya na karkashin ofishinsa na SSG.

“Daga lokacin da mu ka hau mulki, jihar Katsina ta samu Naira biliyan 6.4 na kudin tsaro, akasin abin da Mahadi Shehu ya fada na Naira biliyan 40.” Mustafa Inuwa.

A game da zargin da ake yi na cewa an saye wayoyin daruruwan miliyoyi, Dr. Inuwa ya ce a nan ma karya ce ake yi, abin da aka kashe wajen sayan wayoyi kamar yadda takardu su ka nuna shi ne N2, 420, 000.00

A kan batun masu gadi da aka rika warewa alawus na ban mamaki a cibiyar lantarki ta Lambar Rimi, gwamnatin Katsina ta ce adadin abin da ta batar duka-duka Naira miliyan 15 ne rak.

KU KARANTA: Yadda ake wawaso da kudin gwamnati a Katsina - Shehu

Babu gaskiya a zargin Mahadi Shehu – inji Sakataren gwamnatin Katsina
Sakataren gwamnatin Katsina da mai girma gwamna
Asali: Facebook

Bayan haka SSG ya ce sun daina biyan ‘yan sanda wadannan alawus tun 2017, kuma sun sanar da ma’aikatar gwamnatin tarayya wannan mataki.

Tasiu Dandagoro wanda shi ne kwamishinan ayyuka, ya musanya zargin cewa ya karbi N125, 000, 000 a asusun bankinsa, ya nuna takardu da ke nuna cewa ba a taba turo masa wannan kudi ba.

Tasiu Dandagoro ya ke cewa: “Maganar cewa na karbi N125m a akawun karya ne, N5,000 kurum na samu, sai albashina na N361,270,36 a bankin Ja’iz.”

Kamar yadda mu ka samu labari, Mustafa Kanti wanda ke rike da kujerar kwamishinan cigaban karkara a Katsina, ya ce akwai yiwuwar wannan ‘dan kasuwa ya bayyana a gaban kotu domin ya yi bayani.

Mustafa Inuwa ya kuma bayyana cewa N30, 000, 000 da N10, 000, 000 aka kashe wajen zaman da aka yi da ‘yan bindiga tsakanin 2016 da 2019, ya ce hukumar EFCC ta na da labarin wannan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel