Mawaki Kanye West ya ce zai yi takarar Shugaban kasar Amurka a 2020

Mawaki Kanye West ya ce zai yi takarar Shugaban kasar Amurka a 2020

Shararren mawakin Amurka, kuma babban masoyin shugaba Donald Trump, Kanye West ya sanar da cewa zai fito takarar kujerar shugaban kasa.

Kanye West ya bada wannan sanarwa ne a shafinsa na Twitter kamar yadda mu ka samu rahoto.

Mawakin ya ce zai shiga cikin jerin wadanda za su nemi kujerar shugaban kasar Amurka a zaben da za ayi a karshen shekarar 2020.

Wannan ya na nufin tauraron zai gwabza da shugaban kasa mai-ci watau Donald Trump da kuma ‘dan takarar babbar jam’iyyar hamayya a yanzu, Joe Biden.

West ya yi amfani da shafinsa na Twitter ya rubuta: “Dole mu fahimci girman Amurka ta hanyar yadda da Ubangiji, da hada-kai wajen cin ma burinmu da kuma gina gobe.”

Mawakin ya kara da cewa: “Ina neman kujerar shugaban kasar Amurka”

KU KARANTA: Rashin jituwa ta sa Messi ya fara tunanin tashi daga Barcelona

Mawaki Kanye West ya ce zai yi takarar Shugaban kasar Amurka a 2020
Kanye West
Asali: Instagram

Kawo yanzu ba a tabbatar da cewa aniyar attijirin mawakin ta cika ba domin sai yanzu ne aka ji shi ya na maganar neman mulki a zabe mai zuwa.

A jihohin Amurka da-dama har yanzu wa’adin fitowa takara bai wuce ba tukuna. Masu neman tsayawa takarar shugaban kasa su na da damar sayen fam har yanzu.

Dole Kanye West ya fito zaben na 2020 a matsayin ‘dan takara mai cin-gashin kansa. Yanzu haka manyan jam’iyyun kasar sun fitar da wanda zai rike masu tuta a Nuwamba.

Kafin yanzu Kanye West da mai dakinsa Kim Kardashian West, sun kai wa shugaba Donald Trump ziyara a fadar shugaban kasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel