Harkar siyasa: Jagororin Jam’iyyar APC sun maida yaki zuwa cikin jihohi

Harkar siyasa: Jagororin Jam’iyyar APC sun maida yaki zuwa cikin jihohi

Masu ruwa da tsaki a tafiyar jam’iyyar APC sun karkatar da akalarsu zuwa jihohi domin samun iko ga shugabannin bangarorin jihohi da na kananan hukumomi da kuma unguwanni.

Jaridar The Punch ta fitar da rahoto a ranar 6 ga watan Yuli, 2020, cewa kusoshin APC su na harin siyasar jihohi da na sauran kananan mazabu yayin da ake shiryawa zaben sababbin shugabanni.

Wasu daga cikin shugabannin jihohi na jam’iyyar ta APC su na tare da majalisar NWC – ta – Adams Oshiomhole wanda manyan jam’iyya su ka ruguza su a taron NEC kwanaki.

A daidai wannan lokaci kuma akwai shugabannin jam’iyyar da ba su tare da mutanen Adams Oshiomhole.

Rahotanni sun bayyana cewa a halin yanzu jam’iyyar APC ta na kokarin tantance sunayen ‘ya ‘yanta bayan wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar sun tsere, sauya-sheka ko kuma sun mutu.

Duk da cewa wasu na kokarin hura wuta a sake zaben sababbin shugabannin jam’iyya a jihohi da kanana hukumomi, wasu su na ganin shugabannin rikon kwarya kurum ya kamata a taba.

“Babu gwamna ko jagoran jam’iyya da zai zauna ya na kallo wadanda ba su tare da shi, su zama shugabanni a jam’iyya. Idan mutum ya yi haka, ya kashe siyasarsa da kansa.” Inji wata majiya.

KU KARANTA: Ban ce ba zan yi wa APC kamfe a Edo ba - Gwamna Zulum

Harkar siyasa: Jagororin Jam’iyyar APC sun maida yaki zuwa cikin jihohi
Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole
Asali: UGC

Jaridar ta ce irin wannan rikici na gida ya fi karfi a Zamfara, Ribas, Ogun, Imo, Kwara da jihar Edo.

A Zamfara, APC ta rasa duka kujerun da ta lashe a zaben 2019 saboda rigimar gida. Rikicin magoya-bayan AbdulAziz Yari da Kabiru Marafa ya ki cinyewa har yau duk da an sauke kaf majalisar NWC.

A jihar Ribas inda nan kuma aka hana APC shiga takarar gwamna, sabanin ya na tsakanin Rotimi Amaechi ne da Magnus Abe. Har yanzu kusoshin na APC su na rikici duk da asarar da su ka yi.

A Ogun kuma, tsohon gwamna Ibukunle Amosun ya juyawa APC baya a 2019, ya marawa ‘dan takarar hamayya Adekunle Akinlade a zaben jihar. A karshe APC ce ta yi nasarar gaje kujerarsa.

Ana fama da irin wannan sabani a jihar Kwara duk da APC ta karbi mulki daga hannun daular Bukola Saraki wanda ta dade ta na juya akalar siyasar jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel