Kamar a fim: Yadda jiragen yakin sojoji suka dinga ruwan wuta a wasu maboyar Boko Haram

Kamar a fim: Yadda jiragen yakin sojoji suka dinga ruwan wuta a wasu maboyar Boko Haram

Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta sanar da cewa ta kashe dumbin mayakan kungiyar Boko Haram yayin wani luguden wuta da jiragenta na yaki suka yi a sansanin mayakan da ke Parisu da Bula Bello a dajin Sambisa da ke jihar Borno.

Manjo Janar John Enenche, shugaban sashen yada labaran atisayen rundunar soji, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar da safiyar ranar Litinin.

A cewar Janar Enenche, rundunar soji ta kai harin ne; "ranar 3 ga watan Yuli a cigaba da atisayen rundunar soji na karasa murkushe mayakan kungiyar Boko Haram bayan samun bayanan sirri a kan wasu sansani da mayakan ke buya.

"Rundunar soji ta aika jiragenta na yaki bayan tabbatar da cewa mayakan suna buya a sansani. Jiragen sun yi luguden wuta, sun saki bamabamai da makamai ma su linzami a sansanin.

"Dumbin mayakan kungiyar sun mutu, sannan an lalata sansaninsu yayin ruwan wutar da jiragen suka yi," a cewar wani bangare na jawabin.

Babban hafsan rundunar sojojin sama ta Najeriya, Air Marshal Sadiqu Abubakar, ya jinjinawa dakarun NAF bisa nasarar da suka samu da kuma kwarewar aiki da suke nunawa.

Kazalika, hedikwatar rundunar soji ta bukaci dakarun soji "su kara zage dantse wajen kara kaddamar da manyan hare - hare a kan 'yan ta'adda da sauran dukkan wasu ma su laifi da ke barazana ga zaman lafiya a cikin kasa.

A ranar Juma'a ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa mayakan Boko Haram sun bude wa wani jirgi mai saukan ungulu mallakar Majalisar Dinkin Duniya (UNHAS) wuta a Damasak, a karamar hukumar Mobbar da ke arewacin jihar Borno.

DUBA WANNAN: Takaicin kwace babur: Dan achaba ya cinnawa kansa wuta a ofishin 'yan sanda

Duk da haka, jirgin ya lallaba ya dawo sansaninsa a Maiduguri jim kadan bayan harin da aka kai masa a ranar Alhamis 2 ga watan Yulin 2020.

UNHAS na taimakawa ne wurin rabon abinci da karkashin shirin samar da abinci na duniya a yankin.

HumAngle ta ruwaito cewa an kai hari a jihar Borno, kwana guda bayan Gwamnan jihar, Babagana Zulum ya jagoranci wata tawaga zuwa Damasak don raba wa fiye da gidaje 12,000 da tallafin abinci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel