Kudin tsaro: Mahadi Shehu ya zargi Gwamnatin Katsina da batar da N24.b a iska

Kudin tsaro: Mahadi Shehu ya zargi Gwamnatin Katsina da batar da N24.b a iska

Alhaji Mahdi Shehu, fitaccen ‘dan kasuwa a Najeriya, ya shiga gidan rediyon Freedom da ke jihar Kaduna, inda ya jefi gwamnatin jihar Katsina da zargin batar da kudin tsaro.

Mahdi Shehu ya zargi gwamnatin Rt. Hon. Aminu Bello Masari da bindiga da fiye da Naira biliyan 24 wanda aka warewa jihar domin magance matsalar tsaro.

Wannan Bawan Allah ya bayyana cewa gwamnatin Katsina ta wawuri Naira miliyan 500 daga cikin asusun tsaro, wanda ta ce ta batar wajen taron jam’iyyar APC na kasa a 2018.

Shararren ‘dan kasuwan ya bayyana cewa ya na da hujjoji da ke nuna yadda aka rika sama-da-fadi da kudin da ya kamata ace ayi amfani da su wajen tsare rai da dukiyar mutanen Katsinawa.

A cewar Shehu, gwamnatin mai girma Aminu Masari ta kashe fiye da Naira miliyan 500 da sunan sayen wayoyin salula ga masu mulki a jihar Katsina. Wadannan wayoyi sun tashi a kan kusan Naira miliyan takwas.

Haka zalika ana zargin gwamnatin APC mai-ci a Katsina da fitar da fiye da Naira miliyan 250 wajen daukar dawainiyar malaman addinin musulunci na kungiyar JIBWIS.

A binciken da wannan Attajiri ya ce ya yi, gwamnatin Katsina ta batar da sama da Nira miliyan 600 da sunan albashin masu gadin wurin aikin samar da lantarki da karfin iska a garin Rimi.

Da ya sake fitowa a wani karo a ranar Asabar, Mahdi Shehu ya zargi gwamnatin Katsina da kashe N40m da N21m wajen sayawa hukumar DSS manhaja da kuma gyaran jirgin sojin sama na kasa a 2017.

Tsakanin 2015 zuwa 2018, ‘dan kasuwan ya ce an yi gaba da N4.7b da sunan tallafi ga jami’an tsaro a jihar ta Katsina. Haka kuma an batar da N1.3994b da nufin tallafawa shugaban bataliyar sojojin kasa da ke jihar.

KU KARANTA: An kama matan jagororin sojojin Boko Haram

Kudin tsaro: Mahadi Shehu ya zargi Gwamnatin Katsina da batar da N24.b a iska
Gwamnan Katsina da wasu manyan jiha
Asali: Facebook

Akwai kuma zargin cewa a ranar 15 ga watan Nuwamban, 2017, an ba shugaban hafsun soji Naira miliyan 250 a matsayin kudin daukar kula da walwalarsa.

An yi makamancin wannan barna a 2018 inda ake zargin an fitar N1.968b a asusun kudin tsaro da nufin biyan alawus ga ma’aikatan gidan gwamnatin Katsina, inji Mahadi Shehu.

Irin wannan kula na musamman ga jami'an tsaro ba ta kare ba, inda a Oktoban 2019, gwamnatin Katsina ta ce ta kashe N654m wajen tallafawa kwamishinan ‘yan sanda na jihar.

Akwai zargin cewa an wawuri N1.8b da nufin gyara Ajiwa dam tun 2016. Bayan an yi kasafi da wannan aiki, an yi sama-da-fadi da kudin da sunan wani kamfanin kasar Sin.

Shugaban kamfanin na Dialogue da ke Kaduna, ya ce an zari wasu kudi kusan Naira miliyan 50 da sunan za a biya bashin kudin daki a wasu otel, amma kudin su ka kare a hannun wani jami’in gwamnati.

Wannan dattijo, haifaffen Katsina ya ce a 2018, an zari tsabar kudi har Naira biliyan uku daga asusun SURE-P, ba tare da an bayyana abin da za ayi da wannan makudan kudin ba.

Har yanzu gwamnatin Katsina ba ta maida martani game da wadannan zargi masu nauyi ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel