Ba mu lale maraba da Adeyeye da Ojudu a Jam’iyyar PDP – Ayo Fayose
A ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli, 2020, wani tsohon gwamna da aka yi a jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi magana game da rade-radin da ake yi na sauyin-shekar wasu jagororin APC.
Mista Ayodele Fayose ya bayyana cewa jam’iyyar hamayya ta PDP ba ta bukatar irinsu Sanata Adedayo Adeyeye da Sanata Babafemi Ojudu su shigo cikinta a wannan lokaci.
A cewar tsohon gwamnan, hadimin shugaban kasa, Babafemi Ojudu da tsohon minista Adedayo Adeyeye ba su da wani nauyi a siyasa da har za su taimakawa jam’iyyar PDP a jihar Ekiti.
Sanata Babafemi Ojudu shi ne mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a harkar siyasa, yayin da Sanata Adedayo Adeyeye ya taba rike kujerar ministan ayyuka a gwamnatin tarayya.
Fayose ya ce ko da cewa wadannan jagorori na APC sun samu matsala da gwamna Kayode Fayemi, jam’iyyar PDP ba ta da sha'awar ganin wadannan ‘yan siyasa sun shigo cikinta.
Ayo Fayose ya yi wannan jawabi ne ta bakin mai magana da yawun bakinsa, Lere Olayinka.
Olayinka ya ce: “Bayan cewa ba su da nauyin komai a siyasa, su (Ojudu da Adeyeye), mayaudara ne wadanda ba su da godiya. Bugu da kari, fushin Ubangiji ya kama su saboda kwadayinsu.”
KU KARANTA: Ana sa-in-sa tsakanin Gwamna Fayemi da Ojudu da wasu 'yan APC
Mista Olayinka Lere ya yi wannan jawabi ne domin maida martani ga Sanata Ojudu wanda ya shiga gidan rediyo a garin Ado-Ekiti ya na nesanta kansa da rade-radin komawa jam’iyyar PDP.
Ojudu ya ce: “Ko mutuwa na yi, aka sa tutar PDP a makarata, zan tashi, in keta tutar, in koma.”
Tsohon gwamna Fayose ya yi wa hadimin shugaban kasar raddi, ya kira sa ‘dan dadi-mulki wanda kansa kawai ya sani. Fayose ya ce Ojudu ya yi fada da kowace gwamnati a jihar.
“Ya yi fada da Niyi Adebayo, da ni, da Segun Oni, yanzu ya na fada da Fayemi."
“Wa zai iya masa a jihar Ekiti?” Fayose ya ke tambaya.
“Mu a jam’iyyar PDP babu abin da za mu amfana daga wanda ba ya komai sai rusa gwamnatin Ekiti.” inji Jagoran na PDP.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng