Majalisa za ta binciki shirin ciyar da makarantun Firamare a wasu Jihohi

Majalisa za ta binciki shirin ciyar da makarantun Firamare a wasu Jihohi

Majalisar wakilan tarayyar Najeriya za ta gudanar da bincike na musamman a game da yadda gwamnati ta ke ciyar da ‘yan makaranta kyauta a wasu makarantu da ke fadin kasar.

A ranar Laraba, 1 ga watan Yuli, 2020, kwamitin da ke bibiyar asusun gwamnati ya bukaci gwamnatin tarayya da hukumar NBS ta yi mata bayani game da yadda ake ciyar da yara a makarantu.

Wannan kwamiti ya na zargin cewa akwai alamar tambaya game da alkaluman da gwamnati ta ke fitarwa na yaran da ake ba abinci kyauta a wasu makarantun firamare da ke kasar.

Jaridar Daily Trust ta ce majalisar wakilai ba ta gamsu da alkaluman da ta ke gani daga hannun gwamnatin tarayya daga lokacin da aka kirkiro wannan shiri zuwa yanzu ba.

‘Yan majalisar tarayyar sun nemi hukumar da ke tare alkaluma na kasa watau NBS ta bada bayanin adadin duka ‘daliban da su ke amfana da wannan shiri na ci da ‘yan makaranta.

KU KARANTA: COVID-19: Babu batun bude makarantu a halin yanzu - Gwamnati

Majalia za ta binciki shirin ciyar da makarantun Firamare a wasu Jihohi
Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya
Asali: Twitter

Haka zalika majalisar kasar ta na so a bi diddikin yadda aka bada kwangilar dafa abinci a makarantun firamaren kamar yadda dokokin kasa su ka tanada.

‘Yan kwamitin sun ce akwai bukatar ayi bincike a game da yadda ake dafa abincin ne domin a kare lafiyar ‘dalibai da sauran Bayin Allah da su ke amfana daga wannan tsari.

Shugaban kwamitin, Honarabul Wole Oke na jam’iyyar PDP ya jinjinawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta kirkiro da wannan tsari na ba ‘yan makaranta abinci.

Duk da kokarin gwamnatin tarayyar, Wole Oke ya ce akwai bukatar majalisa ta sa ido wajen duba yadda ake aiwatar da wannan shiri domin ayi maganin barnar dukiyar gwamnati.

Yemi Kale mai tarawa gwamnati alkaluma ya ce ofishinsa zai kawowa majalisar adadin ‘daliban da su ka amfana da tsarin, tare da kuma jerin makarantun da wannan shiri ya ke aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel