Kudin wuta: Shugabannin majalisa sun hadu da Buhari don saukakawa talakawa

Kudin wuta: Shugabannin majalisa sun hadu da Buhari don saukakawa talakawa

Gwamnatin tarayya tare da hadin guiwar majalisar dokokin tarayya sun kammala yarjejeniyar tsayar da karin kudin wutar lantarki da zai fara a watan Yulin 2020.

An cimma yarjejeniyar ne bayan shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasar.

Shugabannin majalisun tarayyar sun yi nasarar shawo kan kamfanonin wutar lantarki da su dakatar da karin kudin wutar da za su yi har zuwa farkon shekarar 2021.

A yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati, shugaban majalisar dattawan ya ce wannan sanarwar ta karin kudin wutar lantarki bai dace ba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kudin wuta: Shugabannin majalisa sun hadu da Buhari don saukakawa talakawa
Kudin wuta: Shugabannin majalisa sun hadu da Buhari don saukakawa talakawa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Lawan ya ce kafin karin, ya kamata a dauki wasu matakai na saka mita ga dukkan masu amfani da wutar, lamarin da yace mataimakin shugaban kasar ya yi maraba da shi.

Ya ce: "Mun ziyarci mataimakin shugaban kasar kasancewarsa daya daga cikin wadanda basu aminta da karin kudin wutar ba.

KU KARANTA KUMA: Rikicin APC: Jam'iyya ta fara sasancin 'ya'yanta da ke fadin kasar

"A ranar Litinin ne shugabannin majalisun tarayyar suka zauna da kamfanin rarrabe wutar lantarki. Mun fahimci cewa lokacin karin kudin wuta bai yi ba.

"'Yan Najeriya na da matsaloli masu tarin yawa a gaban su saboda wannan annobar. A saboda haka ne akwai bukatar daukar kowanne mataki a sannu.

"Tabbas gwamnati na kokari a wannan bangaren amma kamfanonin rarrabe wutar lantarki ya kamata su mutunta jama'a."

Gwamnatin tarayya ta kashe N1.8 tiriliyan a cikin shekaru shida a bangaren wutar lantarki.

A yayin da jami'an gwamnati ke sanar da cewar kudin na tallafi ne, masu gudanar da kamfanonin lantarki masu zaman kansu na cewa bashi aka ba su domin dinke barakar sama da N1.5 triliyan da aka samu a ma'aikatar wutar bayan mayar da ita mai cin gashin kanta a 2013.

Wani bincike na naira triliyan 1.8 din ya nuna cewa babban bankin Najeriya ya bayar da bashin naira biliyan 214 a 2014 ta shirin NEMSF, wanda daga nan ne kamfanin DisCos suka samu naira biliyan 58.

Kamfanonin da suka ci moriyar wannan shiri na biyan CBN bashin da ribar kaso 11 cikin dari duk wata na tsawon shekaru 10.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng