APC: Tinubu, Amaechi, El-Rufai da Fayemi za su koma su wanke allonsu a Jam’iyya

APC: Tinubu, Amaechi, El-Rufai da Fayemi za su koma su wanke allonsu a Jam’iyya

Jagororin jam’iyyar APC sun koma gidan jiya bayan majalisar NEC ta sauke shugabannin jam’iyya na kasa. Yanzu jiga-jigan APC suna sabon lissafin yadda za su karbe jam’iyya.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto a ranar Laraba cewa daga cikin wadanda su ke lissafin 2023 a APC akwai Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Rotimi Amaechi; Nasir El-Rufai; da Kayode Fayemi.

Wani na-hannun daman Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ce mai gidansa ya na tsara yadda za a bullowa 2023 domin kuwa babban ‘dan siyasa ne shi wanda ya san yadda zai wanke allonsa.

Ya ce: “Jagoranmu babban ‘dan siyasa ne, ya san harkar, kuma ya san hannunsa. Shi ne Sanatan da aka fara zaba a Najeriya da kuri’u fiye da miliyan guda a 1993. Mu na da shekaru biyu”

Yaron na Bola Ahmed Tinubu ya ce sun so ace Adams Oshiomhole ya karasa wa’adinsa, amma tun da har shugaban kasa ya yi magana, ba za a ga jigon jam’iyyar ya fito ya na jayayya ba.

A wani gefe guda, gwamnoni Kayode Fayemi da Nasir El-Rufai su na kokarin samun gindin zama da kyau a jam’iyya. Wani na-kusa da gwamnan Ekiti ya ji dadin sauke shugabannin da aka yi.

KU KARANTA: Manyan APC sun rude bayan samun labarin Coronavirus ta kama Akeredolu

APC: Tinubu, Amaechi, El-Rufai da Fayemi za su koma su wanke allonsu a Jam’iyya
Nasir El-Rufai da Kayode Fayemi
Asali: UGC

Magoya bayan Fayemi su na ganin cewa burinsu zai cika idan su ka samu su ka yi karfi a jam’iyyar.

Shi kuma wani ‘Dan-a-mutun ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce APC ta kauce hanya. Ya ce: “Da aka kafa jam’iyyar APC, yarjejeniyar ita CPC za ta rike mulki, ACN za ta rike jam’iyya, sai kuma n-PDP za ta rike majalisa, amma yanzu CPC da ACN su na so su kama ko ina.”

Magoya bayan Amaechi sun shaidawa jaridar cewa ba za su yarda da wannan riko ba ganin an tunkari 2023. Amaechi ya na cikin wadanda shugaba Buhari ya yarda da su daga yankin Kudancin kasar.

Alhaji Abdullahi Gambo Abba, wani jigo na jam’iyyar APC a Kaduna, ya karyata rade-radin cewa Nasir El-Rufai ya na da hannu wajen ruguza NWC, ko ma burin tsayawa takara a zaben 2023.

A cikin wadannan manyan ‘yan siyasa babu wanda ya fito fili ya ce zai nemi kujera a 2023.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel