Za a jawo bututan gas daga Jihar Kogi zuwa Garuruwan Kaduna da Kano - Buhari

Za a jawo bututan gas daga Jihar Kogi zuwa Garuruwan Kaduna da Kano - Buhari

- An fara shirin aikin shimfida bututun gas tun daga Ajaokuta zuwa Kaduna da Kano

- Shugaban kasa ya kaddamar da wannan aiki daga ofishinsa ba tare da ya je filin ba

- Wannan kwangila zai dauki tsawon akalla shekaru biyu ana yi kafin a kammala sa

A yau Talata, 30 ga watan Yuni, 2020, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin jawo karfin gas daga garin Ajaokuta, jihar Kogi zuwa Kaduna da Kano.

Layin gas za su fito daga Ajaokuta zuwa Kaduna da jihar Kano kamar yadda aka bayyana a baya.

Kamar yadda mu ka samu labari daga hadimin shugaban kasa, Tolu Ogunlesi, a lokaci guda aka kaddamar da aikin daga iyakar Rigachukun a jihar Kaduna da kuma Ajaokuta.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da shugabannin majalisar tarayya, Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamilla sun halarci taron kaddamar da aikin a fadar shugaban kasa.

Sauran wadanda su ke halartar wannan biki ta bidiyo sun hada da gwamnonin jihohi, ministocin tarayya da shugabannin hafsun sojin kasar da manyan jami’an hukumomin gwamnatin tarayya.

KU KARANTA: Ranar Talata za a fara aikin kai gas zuwa Kaduna da Kano

Za a jawo bututan gas daga Jihar Kogi zuwa Garuruwan Kaduna da Kano - Buhari
Nasir El-Rufai Hoto: Twitter
Asali: Twitter

A jihar Kaduna, mai girma gwamna Malam Nasir El-Rufai ya halarci bikin kaddamar da aikin daga iyakar Dankande a Rigachikun. Gwamnan ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter dazu.

Da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke magana wajen bikin, ya bayyana aikin da cewa ya na da matukar muhimmanci ga Najeriya.

“Za mu yi wannan gagarumin aiki ne saboda mu bunkasa abubuwan more rayuwarmu. Za mu yi amfani da wannan aiki wajen samar da karfin gas ga kananan ‘yan kasuwa domin zaburar da zimmar kasuwancin ‘Yan Najeriya.”

Shugaban kasar ya ce: “Wannan aiki ya na da matukar amfani ga mutanenmu, dole a ci nasara.”

Shugaban kasar ya ce za a ga tasirin wannan aiki a tattalin arziki ta hanyar samar da aikin yi da inganta masana’antu. Shugaban ya ce wannan ya na cikin alkawarin da ya yi wa ‘yan Najeriya.

Shugaban kamfanin mai na kasa watau NNPC ya halarci bikin ta iyakar Ajaokuta, jihar Kogi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel