Jerin Attajiran ‘Yan wasan kwallon kafan Najeriya da kudin da su ke samu a 2020
Harkar kwallon kafa ta na cikin abin da ke kawo makudan kudi a Duniya. Ba a bar ‘yan wasan Najeriya a baya ba, inda shahararrun ‘yan kwallon kasar su ke wanke biyar, su tsoma goma.
Mun kawo maku jerin ‘yan kwallon Najeriya da irin albashin da su ke samu a kowane wata a kungiyoyinsu da ke kasashen waje. Mun tsakuro wannan bayani ne daga jaridar Pulse.
1. Odion Ighalo
‘Dan wasan aron na Manchester United ya na tashi da £130,000. A kudin Najeriya, hakan ya na nufin N71m su ke shiga hannun Tauraroron duk wata.
2. Victor Moses
‘Dan wasan gaban da ke bugawa Chelsea ya koma kungiyar Inter-Milan inda ya ke samun £110,000 (kimanin N60m) a wata.
3. Wilfred Ndidi
Shararren ‘dan kwallon tsakiyar kungiyar Leicester City ya na da albashin £75,000. A kudin Najeriya, albashin na sa ya haura N40m.
4. Ahmed Musa
Ahmed Musa wanda ke bugawa kungiyar Al-Nassr a Saudi Arabiya ya kan karbi £60,000 (fiye da N30m) a kwantiraginsa.
5. Kelechi Iheanacho
Kungiyar Leicester City ta na biyan tsohon ‘dan wasan gaban Manchester City watau Kelechi Iheanacho fam £60,000 (Kusan N33m) duk wata.
KU KARANTA: Hotunan motoci masu tsada da ke cikin gidan Ahmed Musa
6. Alex Iwobi
Fam £50,000 Everton ta ke biyan ‘dan wasa Alex Iwobi. Tsohon ‘dan wasan na Arsenal ya na cigaba da samun albashin kusan N27m a Ingila.
7. Moses Simon
Tauraro Moses Simon ya na cikin wadanda ke tashi da albashi masu tsoka a 2020. Albashinsa ya kusa kai N20m (€37,500) a Nantes.
8. Ola Aina
Tsohon ‘dan wasan Chelsea, Aina, ya na samun €35,500 (kimanin N17m) a kungiyar Torino.
9. Isaac Success
Duk watan Duniya kungiyar Watford ta kan biya Isaac Success fam £30,000 (kusan N16.5m).
10. Henry Onyekuru
Bayan barin Monaco zuwa Galatasaray a kasar Turkiyya, an cigaba da biyan Henry Onyekuru albashin fam €32, 500 (N16m)
Sauran Taurarin da ke wannan jeri su ne:
11. Victor Osimhen (N12.2m)
12. Kenneth Omeruo (N10m)
13. Leon Balogun (N10m)
14. Anthony Nwakaeme (N8.1m)
15. Willian Troost-Ekong (N7m)
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng