Buni ya roki ‘Ya ‘yan Jam’iyyar APC su janye kara a kotu, zai hadu da Tinubu

Buni ya roki ‘Ya ‘yan Jam’iyyar APC su janye kara a kotu, zai hadu da Tinubu

A halin yanzu jam’iyyar APC mai mulki ta ke yunkurin kashe wutar rikicin da ya barke a cikin-gida, wannan ya sa majalisar koli ta NEC ta nada sababbin shugabanni na riko a kasa.

Rahoton da mu ka samu daga jaridar Punch ya tabbatar mana da cewa sababbin shugabannin rikon kwaryar da aka nada a APC, za su nemi haduwa da jigon jam’iyya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A ranar 29 ga watan Yuni, 2020, jaridar kasar ta ce kwamitin na rikon kwarya zai gana da tsohon gwamnan ne domin ya samu goyon bayansa da na masoyansa.

Ana sa ran cewa hakan zai taimakawa jam’iyyar wajen shawo kan rikicin da ya barke. Bola Tinubu ya na cikin kusoshin da su ka tashi-tsaye wajen ganin an kafa jam’iyyar a 2013.

Majiyar ta ce: “An yarda cewa kwamitin (shugabannin rikon kwarya), ya je ya hadu da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.”

Ya kara da cewa: “Kuma za a lallashe shi, sannan a tabbatar masa da cewa an ruguza majalisar NWC ta Adams Oshiomhole ne ba da nufin kai masa hari ba. Ya na cikin manyan jagororinmu.”

KU KARANTA: Buni ya karbi ragamar APC daga hannun Giadom

Buni ya roki ‘Ya ‘yan Jam’iyyar APC su janye kara a kotu, zai hadu da Tinubu
Alhaji Mai Mala Buni Hoto: APC
Asali: UGC

Kwamitin rikon na APC ya sa ranar da zai gana da Bola Ahmed Tinubu. Kafin yanzu ‘dan siyasar ya nuna cewa ya na goyon bayan matakin da jam’iyya ta dauka a taron NEC.

"Mu na sa ran kai masa ziyara gobe (Talata). Idan ziyarar ba ta yiwu gobe ba, za mu samu mu gana da shi kafin karshen makon nan.” inji majiyar.

Bayan an rantsar da Mai Mala Buni a matsayin sabon shugaban rikon kwarya, ya bayyana cewa ba a sauke shugabannin APC na kasa domin ganin bayan wani babba a jam’iyyar ba.

Yanzu kwamitin Mai Mala Buni ya fara aiki da nufin sasanta ‘ya ‘yan APC a Edo, sannan a maida hankali wajen shirya zaben fitar da gwanin jam’iyya a jihar Ondo.

Gwamnan na jihar Yobe ya kuma yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyya su janye duk wasu kara da su ka kai gaban kotu. Wannan ya na cikin matakan farko da za a bi domin ganin an yi sulhu a APC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel