Ojudu: Gwamna Fayemi ya na kokarin kashe kasuwar jam’iyyar APC a Jihar Ekiti

Ojudu: Gwamna Fayemi ya na kokarin kashe kasuwar jam’iyyar APC a Jihar Ekiti

Wasu manyan jagororin jam’iyyar APC a jihar Ekiti, daga cikinsu har da mai ba shugaban kasa shawara, su na zargin gwamna Kayode Fayemi da yunkurin taka masu ja da shi a tafiyar siyasa.

Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran fusatattun ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a Ekiti har su 16 su na kuka da gwamnan kamar yadda wata takarda da su ka fitar ta nuna.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tunanin jam’iyyar APC ta kama hanyar shawo kan rikicin cikin gidan da ya barke mata, wanda har majalisar koli ta NEC ta sauke shugabannin kasa.

‘Ya ‘yan jam’iyyar sun ce tun da gwamna Kayode Fayemi ya zama gwamna, APC ta jihar Ekiti ba ta kira wani taron siyasa ko aka fita gangami ko kuma aka karbi sababbin shiga jam’iyya ba.

A cewarsu, gwamna Fayemi ya na neman sa kafar wando daya da duk ‘ya ‘yan jam’iyya da ba su tare da shi. Su ka ce gwamnan ya kama hanyar ganin bayan wadannan mutane a siyasance.

Fustattun ‘yan jam’iyyar ta APC sun kuma koka da yadda ake dakatar da wasu daga APC babu gaira babu dalili.

KU KARANTA: Fayemi su na da hannu wajen tsige NWC a APC - Jigon PDP

Ojudu: Gwamna Fayemi ya na kokarin kashe kasuwar jam’iyyar APC a Jihar Ekiti
Gwamna Kayode Fayemi da Sanata Babafemi Ojudu
Asali: UGC

‘Ya ‘yan jam’iyyar su ka ce: “A cikin kusan shekaru biyu, jam’iyya ba ta shirya taron masu ruwa da tsaki ba, babu karbar sababbin shiga, babu wani sha’ani na siyasa domin a kara tabbatar da karfin APC a jihar tun da gwamnatin nan ta soma har zuwa yanzu.”

“A maimakon kara yawa, ‘ya ‘yan jam’iyya raguwa su ke yi duk rana.” A cewar 'yan jam'iyyar.

Bayan haka, kusoshin jam’iyyar mai mulki sun ce babu wani aikin kirki da gwamnatin Kayode Fayemi ta dauko tun daga lokacin da ta karbi mulkin jihar Ekiti har zuwa yau.

Kalubalen bai kare a nan ba, wadannan mutane sun bukaci gwamna Fayemi ya bayyanawa jama'a irin kokarin da gwamnatinsa ta ke yi na yaki da annobar cutar COVID-19 a Ekiti.

A daidai lokacn da shugaban kasa da majalisar NEC ta ke kira ga duk ‘ya 'yan jam’iyya su ajiye kayan yakinsu, hadimin shugaban kasar da mutanesa ba su da niyyar saurarawa Fayemi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel