Ku tsamo 'yan bindiga tare da karar da su - Masari ga rundunar soji

Ku tsamo 'yan bindiga tare da karar da su - Masari ga rundunar soji

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari ya bai wa rundunar soji umarnin gamawa da 'yan bindiga da ke kashe 'yan jihar. Ya kara da cewa kada a bar dan bindiga ko daya da rai.

Masari ya yi wannan kiran ne yayin da ya kai ziyara ga 'yan gudun hijira a kananan hukumomin Faskari, Kadisau da Dandume na jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ya ce: "Akwai bukatar a kawar da 'yan bindigar kwata-kwata daga jihar don samun dawowar zaman lafiya."

"Yare daya ne 'yan bindigar ke fahimta. Harbi da AK 47, don haka da shi za a karar da su tunda sun fi gane shi."

Ku tsamo 'yan bindiga tare da karar da su - Masari ga rundunar soji
Ku tsamo 'yan bindiga tare da karar da su - Masari ga rundunar soji Hoto: Independent
Asali: UGC

Ya tabbatar da cewa 'yan gudun hijira 4,000 ne suke makarantar firamare na Faskari da kuma 800 a karamar hukumar Dandume.

Ya ce za su ci gaba da bada kula mai inganci ta hanyar samar musu da kayan abinci da magani yayin zaman da za su yi a sansanin.

KU KARANTA KUMA: Kaduna: An tsinci gawar yarinya mai shekaru 6 da aka yi wa fyade a masallaci

Ya kara da cewa an tura dakarun soji da 'yan sanda don su shawo kan matsalar 'yan bindiga. Babu dadewa 'yan gudun hijira za su koma gidajensu tare da komawa ayyukansu na noma.

A yayin kushe mummunan aikin 'yan bindigar, ya tabbatar da cewa za a zakulo masu kai wa 'yan bindigar bayanai sannan su fuskanci hukunci irin na 'yan bindigar.

Kwamishinan wasanni da matasa, Alhaji Sani Danlami ya sanar da gwamnan cewa an kafa kwamiti don ciyarwa tare da samar da magani ga 'yan gudun hijira a sansanin Faskari da Dandume.

Ya sanar da cewa wasu 'yan siysa na tallafawa ayyukan gwamnatin jihar ta yadda suke bada tallafin kayan abinci ga 'yan gudun hijirar.

A karamar hukumar Faskari, Alhaji Lawal Ibrahim Danmummuni ya sanar da gwamnan cewa sansanin ya cika fal bayan harin da 'yan bindigar suka kai Kadisau a ranar 9 ga watan Afirilu.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa da yawa daga cikin 'yan gudun hijirar da ke samun mafaka a sansanin 'yan gudun hijira da ke Faskari a jihar Katsina sun rushe da kuka yayin da gwamna Aminu Masari da wasu manyan jiga-jigan gwamnati suka kai ziyara sansanin.

Sun bukaci tallafi sakamakon ibtila'in da ya fada musu.

Yara da mata sun fashe da kuka bayan da gwamnan tare da manyan jami'an gwamnati suka bar sansanin bayan ziyarar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel