Edo 2020: Ize-Iyamu za mu zaba ba Obaseki ba duk da ina ‘Dan PDP – Inji Afegbua

Edo 2020: Ize-Iyamu za mu zaba ba Obaseki ba duk da ina ‘Dan PDP – Inji Afegbua

Jagoran PDP a jihar Edo, Prince Afegbua Kassim, ya sha alwashin hada-kai da APC wajen ganin Godwin Obaseki ya sha kashi a zaben gwamna da za ayi a jihar Edo a Satumban 2020.

Jaridar Vanguard ta rahoto Prince Afegbua Kassim ya na sukar gwamna mai-ci Godwin Obaseki saboda yadda ya ke neman komawa kan kujerar mulki ido rufe bayan ya bar APC.

‘Dan siyasar ya soki jam’iyyarsa a kan yadda ta ba Godwin Obaseki tikiti bayan ya soki PDP baya.

“Za mu hada kai da ‘dan takarar APC, mu tabbatar cewa Godwin Obaseki bai koma mulki ba. Ni ‘Dan PDP ne, amma jam’iyyar APC zan zaba.” Inji Mista Prince Afegbua Kassim.

Ya ce: “Mutum irin Fasto Osagie Ize-Iyamu ya fi gwamnan da ya ke fada da duk wanda ya samu jayayya da shi. An raba kan jihar Edo sosai saboda rigingimu na babu gaira, babu dalili”

KU KARANTA: Buhari bai san shirin da wasu Gwamnonin APC su ke yi ba – Afegbua

Edo 2020: Ize-Iyamu za mu zaba ba Obaseki ba duk da ina ‘Dan PDP – Inji Afegbua
Gwamna Godwin Obaseki Hoto: PDP
Asali: Twitter

“Ya kamata mu samu sabon shugabanci da zai kawo zaman lafiya ga kowa. Surutan da ake yi a dalilin takarar Obaseki ya rikita ko ina, kuma ba don talaka ake yi ba.”

Tsohon kwamishinan ya bayyana cewa bai kamata a ce Omoregie Ogbeide-Ihama ya janye takararsa ba. “Siyasar kudi wanda ta zama mana matsala a kasa ce ta hadiye Hon. Ogbeide-Ihama.”

Afegbua Kassim ya zargi gwamna Obaseki da amfani da kudin wajen sayen tikitin takararsa a PDP.

Haka kuma ya cigaba da sukar gwamnan mai-ci da ya dawo PDP kwanan nan: “Ta ina wanda bai saye fam din takara ba, wanda ya shigo a lokacin da aka gama saida fam, ya murde ‘ya ‘yan jam’iyya, ya zama ‘dan takara?”

“Gwamnan da ya zargi tsofaffin shugabanninsa na APC da rabawa ‘yan jam’iyya kudi, ya zo PDP ya yi irin abin da ya ke korafi a kai. An rabawa ‘yan jam’iyya kudi, an saye takara.” Afegbua ya ce wannan abin kunya ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel