Afegbua: Harin 2023 ya ci Adams Oshiomhole har ya bar shugabancin jam’iyyar APC

Afegbua: Harin 2023 ya ci Adams Oshiomhole har ya bar shugabancin jam’iyyar APC

- Prince Kassim Afegbua ya fadi abin da ya jawo APC ta rusa Majalisar NWC

- ‘Dan adawar ya ce wasu manya su ka sa aka yi waje da Adams Oshiomhole

- A cewarsa, wadannan manyan Gwmanoni na APC su na harin takara a 2023

Wani daga cikin jagororin jam’iyyar hamayya a kudancin Najeriya, Prince Kassim Afegbua, ya sa baki a rigimar cikin gidan da ake yi a APC, wanda har ya kai aka sauke shugabanni na kasa.

Mista Prince Kassim Afegbua ya na ganin cewa an sauke Adams Oshiomhole da majalisarsa ne saboda harin siyasar 2023 inda za a samu sababbin zubin ‘yan takarar shugaban kasa a APC.

Kassim Afegbua ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yi wata hira da jaridar Vanguard a jiya.

“Babu wani abin a zo – a gani game da sallamar Adams Oshiomhole daga jam’iyya. Lissafin 2023 ce ta sa ya rasa kujerarsa, musamman ga wadanda su ke ganin zai yi masu taurin juyawa.” Inji sa.

Tsohon kwamishinan na jihar Edo, Afegbua ya zargi wasu gwamnonin APC da wannan aiki.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa Buhari ya juya baya ga Shugabannin APC

Afegbua: Harin 2023 ya sa Adams Oshiomhole ya bar shugabancin jam’iyyar APC
Prince Kassim Afegbua
Asali: UGC

“Shugaban kasa bai iya fahimtar siyasar da aka bugawa ba. Ka na da gwamoni irinsu Atiku Bagudu na Kebbi, Nasir El-Rufai na Kaduna, Abubakar Badaru na Jigawa, Kayode Fayemi na Ekiti da Simon Lalong na jihar Filato wadanda ya kamata su tsaya su yi aiki, amma su na hangen takarar 2023.” Inji Kassim Afegbua.

A cewar Prince Kassim Afegbua, wadannan gwamnoni biyar da su ke wa’adin karshe su na da burin fitowa takarar shugaban kasa a zaben 2023 a karkashin jam’yyar APC mai mulki.

‘Dan siyaar ya kuma caccaki jam’iyyarsa a dalilin tsaida Godwin Obaseki a matsayin ‘dan takararta a zaben Edo. Afegbua ya yi tir da yadda idanuwan gwamnan da jam’iyyarsa su ka rufe.

Idan ba ku manta ba a makon jiya ne jam’iyyar APC ta rusa majalisar NWC a wajen taron NEC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng