Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya ɗaga taronsa a NEC saboda zaman APC

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya ɗaga taronsa a NEC saboda zaman APC

Jaridar The Cable ta ce mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya dakatar da taron da ya shirya zai yi a majalisar tattalin arziki na kasa a ranar Alhamis.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada sanarwar cewa zai halarci taron NEC na jam’iyyar APC wanda Victor Giadom ya sa a yau da rana.

Shugaban kasar ya marawa mataimakin sakataren jam’iyyar APC na kasa, Victor Giadom wanda yanzu ya ke cikin masu ikirarin rike kujerar shugaban jam’iyya na rikon kwarya.

A dalilin taron jam’iyyar, Farfesa Yemi Osinbajo ya dakatar da wannan zama da aka shirya sai wani lokaci nan gaba kamar yadda ya sanar ta bakin sakataren majalisar ta NEC.

Olusola Idowu ya shaidawa gwamnoni a madadin Yemi Osinbajo cewa za a fitar da ranar da za ayi taron NEC na 105. Lokaci bayan lokaci, majalisar ta kan zauna a fadar shugaban kasa.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun rufe ofishin APC ana shirin taron NEC

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya ɗaga da taronsa a NEC saboda zaman APC
Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: Ofishin VP
Asali: Twitter

“Shugaban majalisa, mai girma Farfesa Yemi Osinbajo, SAN, GCON, ya bada umarni in shaida cewa an ɗaga taron NEC da aka shirya za ayi ta kafar yanar gizo a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni, 2020.”

Jawabin Mista Olusola Idowu ya kara da cewa: “Za a sanar da ku ranar da za ayi wannan taro.” Sannan ya ce: “Mu na matukar bada hakurin matsalar da wannan mataki da aka dauka ya jawo maku.”

Ana sa ran cewa wasu Ministoci, gwamnan CBN, da gwamnonin APC, wanda wasunsu su na cikin majalisar tattalin arziki da Yemi Osinbajo ya ke jagoranta za su halarci taron NEC da za a yi an jima.

Shugaban majalisar tarayya da wasu jagorori a majalisa su na cikin wadanda aka gayyata wannan taro. Amma kuma rahotanni na zuwa cewa jami'an tsaro sun garkame ofishin jam’iyyar APC dazu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng