APC NEC: Karfe 12 na rana Buhari zai shiga taron jam'iyya

APC NEC: Karfe 12 na rana Buhari zai shiga taron jam'iyya

- Jam'iyyar APC za ta gudanar da babban taro na shugabanninta a yau Alhamis, 25 ga watan Yuni, da misalin karfe 12:00 na rana

- Daga cikin manyan da za su halarcci taron harda shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Mataimakin sakataren jam'iyyar na kasar, Victor Giadom ne ya kira taron bayan zama mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa da yayi

- Sai dai kuma da yawa daga cikin 'yan kwamitin gudanar da ayyukan jam'iyyar sun soki taron don sun ce Giadom bashi da hurumin kiransu taro duk da cewa shi ba mamba bane a kwamitin

Shugabannin jam'iyyar APC za su shiga taro da karfe 12 na ranar yau, Alhamis, 25 ga watan Yuni, a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke Aso Villa da ke Abuja, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Mataimakin sakataren jam'iyyar na kasar, Victor Giadom ne ya kira taron bayan zama mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa da yayi.

Tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai samu halartar taron. Ya yi kira ga gwamnoni da sauran shugabannin jam'iyyar da su halarta.

Wannan taron ne babban yunkuri na biyu da aka yi don kawo sasanci a rikicin jam'iyyar.

Da yawa daga cikin 'yan kwamitin gudanar da ayyukan jam'iyyar sun soki taron don sun ce Giadom bashi da hurumin kiransu taro duk da cewa shi ba mamba bane a kwamitin.

APC NEC: Karfe 12 na rana Buhari zai shiga taron jam'iyya
APC NEC: Karfe 12 na rana Buhari zai shiga taron jam'iyya Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Shugabannin sun hada da sakataren jam'iyyar, Waziri Bulama da kakakin jam'iyyar Lanre Issa-Onilu. Sun nuna alamun cewa ba za su halarci taron ba duk da shugaban kasa ya nuna goyon baya.

KU KARANTA KUMA: Daga karshe: Kotu ta sa ranar yanke hukunci a kan kisan 'yan shi'a

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana goyon bayan sa a kan taron inda ya ce doka na bayan Victor Giadom a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa.

Duk da har yanzu ba a san abinda za a tattauna a taron ba, Premium Times ta gano cewa akwai yuwuwar a sauke kwamitin gudanar ayyukan jam'iyyar wanda ya rabu kashi-kashi.

A yayin da aka nemi jin ta bakin kakakin jam'iyyar, Issa-Onilu,ya ki daukar wayarsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel