Kayode Fayemi ya karyata zuwa wurin Shugaban kasa tare da Victor Giadom

Kayode Fayemi ya karyata zuwa wurin Shugaban kasa tare da Victor Giadom

Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti, ya zargi mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kan harkar siyasa watau Sanata Babafemi Ojudu, da yi masa sharri.

Dr. Kayode Fayemi ya ce maganar cewa ya nemi ya gana da mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya saida masa takarar Victor Giadom ba gaskiya ba ne.

A rahotannin da aka fitar, an ce ba a ba gwamnan damar ganin shugaban kasar a Aso Villa ba.

Mai magana da yawun bakin gwamnan Ekiti, Yinka Oyebode, ya yi maza ya karyata wannan rahoto, ya ce Babafemi Ojudu ne ya kitsa wannan labari domin ya ci mutuncinsa.

Mista Yinka Oyebode ya ce Babafemi Ojudu ya na aiki ne a karkashin ofishin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

A cewar hadimin gwamnan, a matsayinsa na shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi ya yi gum da bakinsa a game da rikicin da ake fama da shi a jam’iyyar APC.

Oyobode ya ce kafin nan Fayemi ya samu damar ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da wasu gwamnonin jihohi uku, bayan nan kuma ya zauna da Ibrahim Gambari.

KU KARANTA: Gwamnonin APC sun gana da Jagoran Jam'iyyar Bola Tinubu

Kayode Fayemi ya karyata zuwa wurin Shugaban kasa tare da Victor Giadom
Kayode Fayemi, Gwamnan Ondo da Buhari
Asali: Depositphotos

Duk a wadannan zama da ka yi, gwamnan bai dauki Victor Giadom zuwa gaban shugaban kasa ko shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasar kamar yadda ake rade-radi ba, inji Oyobode.

Jawabin gwamnan ya ce:

“Hankalinmu ya zo kan wani labarin karya da aka wallafa da taken cewa ‘Ziyarar Fayemi da Giadom a fadar shugaban kasa ta ci tura’ a kafar yanar gizo a ranar Laraba, 24 ga watan Yuni, 2020.”

“Mun samu labari daga majiya mai karfi cewa babban hadimi a fadar shugaban kasa kuma tsohon Sanata, Babafemi Ojudu ne ya shirya wannan karya, ya kafa a gidan jaridar The Nation, bayan ‘yan jaridar fadar shugaban kasa sun yi watsi da rahoton na bogi.”

“A sani cewa Sanata Ojudu a yunkurinsa na bata gwamna Fayemi, ya sha alwashin sai ya ci mutuncin gwamnan wanda shi ne shugaban kungiyar NGF domin hargitsa jam’iyyar APC a Ekiti.

Jaridar TheCable ta nemi jin ta bakin Ojudu, inda ya karyata jawabin gwamnan. “Wannan karya ce, babu dalilin in maida martani. Kamar yadda Socrates ya fada, inda an rasa abin fada, sai a koma sharri.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel