Rikicin APC: Wasu kusoshin da aka kafa Jam’iyya da su za su halarci taron NEC

Rikicin APC: Wasu kusoshin da aka kafa Jam’iyya da su za su halarci taron NEC

Jaridar Daily Trust ta ce wasu daga cikin jagororin da aka kafa jam’iyyar APC da su a Najeriya, sun goyi bayan taron majalisar NEC da aka kira a yau Alhamis, 25 ga watan Yuni, 2020.

Jagororin jam’iyyar APC da su ka sa hannu a wannan jawabi da ya nuna goyon bayansu da amsa goron gayyatar wannan taro sun hada da Salihu Mustapha, Polycap Udah, Capt Bala Jibrin, Ray Morphy, da Umar Kachalla Zubair.

Sauran wadanda za su halarci taron majalisar zartarwar su ne: Dr Slyvanus Amechi, Shaba Emangi, Emeka Enechi, Charles Idahosa, Mohammed Aboki Mahmud. Sai kuma Prince Maxkor Shaka Momodu da Yusuf Omobeni.

‘Ya ‘yan jam’iyyar sun yi kira ga duk wadanda ke cikin majalisar NEC, su ajiye bambancin ra’ayi a gefe, su halarci wannan muhimmin taro domin ceto jam’iyyar daga cikin halin da ta samu kanta.

Ga abin da jawabin ya ce:

"Mu a matsayinmu na wakilan wadanda aka kafa jam’iyyar APC da su daga tsofaffin jam’iyyun da su ka narke, mu na murna hannu biyu-biyu da taron NEC da aka shirya za a yi a ranar 25 ga watan Yuni 2020 domin a ceci jam’iyyar.”

KU KARANTA: APC: Giadom ya na tsoron wasu ba za su halarci taron NEC ba

Rikicin APC: Wasu kusoshin da aka kafa Jam’iyya da su za su halarci taron NEC
Victor Giadom Hoto: APC
Asali: UGC

Wadannan tsofaffin jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki sun ce taron na NEC ya zama dole.

Jawabin kusoshin jam’iyyar ya kara da cewa: “Mu na kira ga duk ‘yan majalisar NEC su halarci wannan taro da za a yi ta kafar yanar gizo ko duk yadda ta kama domin a ceci jam’iyyarmu.”

Su ka ce: “Wannan taro ya zama dole – a cikin babin lalura, kuma shi ne damar karshe na ceto kurwar jam’iyyar APC; saboda mun koka sosai a game da abin da ya ke faruwa da jam’iyyarmu na rasa gwamnoni 23 a (zaben) 2019, inda yanzu babu wanda ya san ina aka dosa.”

“Kuma abin takaici, jam’iyyar hamayyar PDP wanda a 2019 ta ke fama da kanta raga-raga, ita ce ke cin moriyar abin da ya ke faruwa yau (a jam'iyyar APC). Wannan ya sa shugabanta Uche Secondous ya kira Adams Oshiomhole sinadarin numfashinsu.” inji ‘yan siyasar.

Jagororin na APC sun nakalto sashe na 13.1 na dokokin jam’iyyar APC a matsayin hujjar wannan zama. Ana tunanin Magoya-bayan Bola Tinubu da 'Yan NWC ba za su halarci taron ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng