Obaseki: Hukumar INEC za ta yi wa kotu biyayya a zaben Jihar Edo
Hukumar zabe na kasa watau INEC ta yi magana game da hukuncin da kotu ta yi game da shigan gwamna Godwin Obaseki neman takarar tikitin jam’iyyar PDP a zaben jihar Edo.
A cewar babban jami'in da ke magana da bakin hukumar, INEC ta ce za ta yi wa kotu biyayya a zaben fitar da ‘dan takarar jam’iyyar PDP da za ayi a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni, 2020.
INEC ta gamsu da hukuncin da Alkali E.A. Obile ya yanke jiya, inda ya yi fatali da takunkumin da aka kakabawa Godwin Obaseki na neman tikitin PDP jim kadan bayan ya sauya-sheka.
Kotu ta ba Godwin Obaseki damar shiga cikin masu neman tikitin PDP ne yayin da ake saura sa’a 48 rak a shiga filin zabe. Wannan hukunci ya zo wa gwamnan mai neman tazarce da sa’ida.
INEC mai gudanar da zabe a Najeriya ta ce za ta yi biyayya ga duk wani hukunci da kotu ta yi, tare da cewa irin wadannan hukunci za su iya kawo cikas wajen zaben tsaida ‘dan takara.
Hukumar ta yi wannan magana ne ta bakin kakakinta, Festus Okoye, a ranar Talata. Festus Okoye ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi magana da jaridar Leadership.
KU KARANTA: 'Yan PDP su na neman jawowa Obaseki biyu-babu a zaben Jihar Edo
Okoye ya ce sun zauna a ranar Talata, inda su ka tattauna game da batutuwa da-dama, daga ciki har da maganar gudanar da zaben tsaida ‘dan takarar PDP a zaben gwamnan jihar Edo.
“Hukumar ta na lura sosai da abubuwan da ke faruwa a jam’iyyu game da shirya zaben fitar da gwani, fito da ‘yan takara, tare da jan-kunnen cewa zuwa kotu za su kawo cikas a zaben.”
“Za a rufe karbar ‘yan takara ne a ranar Litinin 29 ga watan Yuni, 2020 da karfe 6:00.” Inji Okoye.
Ya ce: “Don haka INEC za ta yi biyayya ga duk wani hukunci da aka samu daga kotu mai iko kamar yadda doka ta tanada.”
Wani mai neman tikiti a jam’iyyar PDP, Omoregie Ogbeide-Ihama, shi ne ya kai kara gaban kotu inda ya bukaci a dakatar da gwamna Obaseki daga shiga zaben tsaida ‘dan takara.
Ogbeide-Ihama ya yi korafin cewa gwamna Obaseki wanda ya dawo PDP a karshen makon jiya bai saye fam a lokacin da aka kayyade bayyana sha’awar neman tsayawa takara ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng