Siyasa: Shugaban Najeriya Buhari ya cirewa Gwamnoni takalman karafuna

Siyasa: Shugaban Najeriya Buhari ya cirewa Gwamnoni takalman karafuna

Gazawar gwamnoni wajen ceton takwaransu Godwin Obaseki a siyasar jihar Edo, inda ta kai dole ta sa ya bar jam’iyyar APC ya nuna yadda gwamnoni su ke rage karfi inji jaridar Daily Trust.

A baya an san gwamnoni da kungiyarsu da samun damar juya akalar tafiyar siyasa, a wannan gwamnati ta APC mai-ci, karfin wadannan gwamnonin jihohi da aka kasance ana damawa da su, ya ragu sosai.

A gwamnatocin baya da aka yi, gwamnoni sun kasance su na da ta-cewa, su rika fadan yadda za a yi a jihohinsu da kuma tarayya, su kuma tsoma baki a cikin siyasarsu ta cikin gida da fadar shugaban kasa.

Wannan karo, shugaban gwamnonin jam’iyyar APC, Atiku Bagudu ya yi ta kai-komo tare da wasu gwamnoni bakwai wajen ganin Abokin aikinsu, Godwin Obaseki, ya samu damar neman tazarce a jam’iyyar APC.

Gwamnonin APC sun yi kokarin ganawa da Asiwaju Bola Tinubu a Legas da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban birnin tarayya Abuja, amma a karshe hakarsu, ba ta cin ma ruwa ba.

KU KARANTA: Buhari ya zai tafi da bangaren Giadom a rikicin Jam'iyyar APC

Siyasa: Shugaban Najeriya Buhari ya cirewa Gwamnoni takalman karafuna
Shugaban kasa Buhari da wasu manyan APC
Asali: UGC

Ba gwamna Obaseki na jihar Edo ba ne farau, a 2018 Akinwumi Ambode ya gamu da irin wannan matsala a Legas. Rikicin gwamna Ambode da Bola Tinubu ya jawo APC ta hana sa neman tazarce.

Jam’iyyar APC ta bankara gwamnan Legas a wancan lokaci da kuma takwarorinsa, inda ta bada tikiti ga Babajide Sanwo-Olu wanda shi ne gwamna mai-ci a yanzu bayan ya lashe babban zabe.

Jaridar ta ce daga shekarar 1999 da aka kafa kungiyar gwamnoni ta NGF wanda gwamna Abdullahi Adamu ya fara jagoranta, NGF ta rika samun damar cin karenta babu babbaka a baya.

Wannan kungiya ta taimakawa gwamnoni wajen sa-hannu a nadin ministoci, kawo sunayen wadanda za a ba mukamai a gwamnatin tarayya, da kuma tsoma baki a sauran wasu harkoki.

Bayan hawan Muhammadu Buhari shugaban kasa a 2015, abubuwa sun fara canzawa gwamnoni zani, inda ya fadawa gwamnonin APC cewa ba za su zaba masa ministocin da zai tafi da su ba.

A kwanaki gwamnonin sun sake yin yunkurin tsige shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, a nan ma ba su yi nasara ba. Wannan ya nuna yadda ake dakile fuka-fukan da su ke tashi da su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel