Zaben Edo: Jagororin PDP ba su goyon bayan a ba Obaseki tikiti da karfi da yaji

Zaben Edo: Jagororin PDP ba su goyon bayan a ba Obaseki tikiti da karfi da yaji

Yayin da ake shirin zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP a jihar Edo, wasu daga cikin masu fada-a-ji a PDP sun nuna adawarsu ga yunkurin da ake yi na fifita gwamna Godwin Obaseki.

Jaridar Vanguard ta zargi uwar-jam’iyyar PDP mai hamayya da nuna fifiko a kan takarar Godwin Obaseki wanda ya sauya-sheka ya dawo tafiyar jam’iyyar daga APC a cikin ‘yan kwanakin nan.

Wadannan ‘ya ‘yan jam’iyya sun bayyana cewa budawa gwamna mai-ci hanya ya sabawa doka.

Majiyar jaridar ta ce wani daga cikin manyan PDP ya na kukan rashin adalci da kin bon doka a jam’iyyar. Ya ce ba ya adawa da sauya-shekar gwamnan, amma akwai bukatar a bi ka’idoji.

A cewarsa, tun farko bai dace a saidawa gwamna Obaseki fam din takara ba ganin cewa lokaci ya kure. Jagoran adawar ya ce a dalilin haka, an take ‘yan siyasa irinsu Ogbeide Omorogie Ihama.

“Abin farin ciki ne na cewa gwamna ya dawo PDP, matsalar ita ce uwar-jam’iyya ta na kokarin kakaba gwamnan a kan wadanda su ka dade a cikin jam’iyya kuma su ka yi aiki dare da rana.”

KU KARANTA: Gwamnonin Neja-Delta za su tashi tsaye su marawa Obaseki baya a Edo

Zaben Edo: Jagororin Jam’iyya ba su goyon bayan a ba Obaseki tikiti a PDP
Godwin Obaseki Hoto: PDP
Asali: Twitter

“Shugabannin PDP da ba za su san siyasar cikin gidarmu ba su na neman kawo matsala saboda zari. Wasu sun yi wa jam’iyya aiki na shekaru, sun bi duk matakan da ake bi na neman takara.

Wannan Bawan Allah ya shaidawa jaridar ko da an ba Obaseki damar neman takara a PDP, sai an tuntubi ‘yan jam’iyya domin gudun a jawo rashin jituwa, saboda ka da wasu su sauya-sheka.

Segun Bakare wanda jagoran PDP ne a Akoko-Edo, ya fito ya na cewa: “Ta ya aka saidawa gwamna Godwin Obaseki fam din nemam takara bayan kwanaki 18 da kammala saidawa?”

“A wani dalili aka ba shi (Godwin Obaseki) damar yankan fam, aka tantancesa, kuma aka ba shi damar ya shiga neman takara ana daf da shirya zaben fitar da gwani.” Inji Segun Bakare

Wani ya ce akwai wasu mutum uku da ke neman gwamna a PDP, kuma sun shafe fiye da shekara guda su na tallar kansu, amma a rana guda, ana neman watsi da su, a kawo wani ‘dan takarar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel