Yahaya Bello: Na ji tausayin Gwamna Obaseki, amma APC za ta lashe zabe a Edo
A ranar Litinin, 22 ga watan Yuni, 2020, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya fito ya yi magana game da zaben jihar Edo. Gwamnan ya ce ya tausayawa abin da ya faru da Godwin Obaseki.
Yahaya Bello ya bayyana cewa duk da tausayin Gwamna Godwin Obaseki da ya ke ji, wannan ba zai hana jam’iyyar APC cigaba da mulki a Edo ba, har ma da hangen APC ta mamaye wasu jihohi.
Bello ya ke cewa karfin mulki ba zai hana APC karbe jihar Edo daga hannun Godwin Obaseki ba. A cewarsa masu rike da mulki sun sha kasa a zaben kasa, daga cikinsu har da Goodluck Jonathan.
Gwamnan ya yi magana da ‘yan jarida ne bayan wata zama da gwamnonin jihohin Arewa ta tsakiya su ka yi da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari a jiya.
Alhaji Bello ya nuna sa ran cewa jam’iyyar APC za ta karbe jihar Anambra bayan Edo. “Jam’iyyarmu ta na nan da karfi sosai. A taro irin wannan, ba ka yin watsi da sabani nan da can.”
Gwamnan ya kara cewa: “Amma ina mai tabbatar maka da cewa jam’iyyarmu ta na da karfi a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari, kuma a matsayinsa na Uba, ya na duba matsalar.”
KU KARANTA: Magoya bayan Gwamna Akeredolu sun gamu da harin 'Yan daba
“Za mu je jihar Edo, za mu ci zabe da kyau, za mu tafi zaben jihar Ondo kuma mu samu gagarumar nasara a APC. Za mu karbe Anambra, ta zama jiha ta biyu a Kudu maso Gabas da ke hannun jam'iyyar APC.”
Da aka tambayi Bello ko ya na tsoron karfin gwamnati mai ci a jihar Edo, sai ya ce: “Mun gani a baya inda aka tika masu mulki da kasa, mun ga yadda Muhammadu Buhari ya kifar da Goodluck Jonathan.”
Bayan haka, gwamnan na Kogi ya ce jihohon Osun da Ekiti ba za su bar hannun jam’iyyar APC ba.
A daidai wannan lokaci kuma Daily Trust ta ce gwamnonin Kudu maso Kudu sun yi taro a karkashin gwamna Ifeanyi Okowa inda su ka cin ma matsayar marawa tazarcen Godwin Obaseki baya a PDP.
Ifeanyi Okowa ya ce gwamnonin yankin sun zabi su goyi-bayan takawaransu a zaben gwamnan da a za ayi a Edo. Okowa ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a Edo, su tashi su yi wa tazarcen Obaseki aiki.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng