Sabon harin Zamfara: Mazauna yankin sun birne mutum 23

Sabon harin Zamfara: Mazauna yankin sun birne mutum 23

Yawan mutanen da suka rasu sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai yankin Ruwan-Tofa na jihar Zamfara ya kai 23, mazauna yankin suka tabbatar.

Mazauna yankin sun ce sun gano za a kai musu harin ana saura kwanaki uku amma sun sha mamaki yadda jami'an tsaro suka ki kai musu dauki duk da sanar dasu da suka yi.

Da farko jaridar Premium Times ta ruwaito cewa a kalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu a yankin Dansadau da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

A yayin tabbatar da aukuwar harin daga rundunar 'yan sanda a ranar Lahadi, rundunar ta ce rayuka 10 aka rasa.

Mazauna yankin sun ce wadansu da suka samu raunika aka kwantar da su a asibiti sun rasu daga baya. Yayin da gawawwakin wadansu aka tsintosu a daji.

Sabon harin Zamfara: Mazauna yankin sun birne mutum 23
Sabon harin Zamfara: Mazauna yankin sun birne mutum 23 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Sama da mutum 12 a halin yanzu ke asibiti inda suke karbar taimakon likitoci a asibitin Dansadau.

Harin na daya daga cikin mafi muni da 'yan bindigar suka kai a cikin shekaru uku, wani mazaunin yankin mai suna Mu'azu Yusuf ya tabbatar.

Yusuf ya ce Ruwan-Tofa ba kamar sauran yankunan DanSadau yake ba don sadaukantakar mazauna yankin yasa 'yan bindigar basu iya kai musu hari.

Ya ce a shekaru uku da suka gabata wasu 'yan bindiga sun kai hari Ruwan-Tofa amma rundunar soji tare da hadin kan 'yan banga suka yi musu kaca-kaca.

Ya tabbatar da cewa mazauna yankin sun ji labarin za a kai musu harin kuma sun sanar da hukumomin da suka dace. Ya jajanta cewa babu abinda aka yi don dakile harin.

"Da kaina na kira kwamishinan tsaro na jihar, Abubakar Dauran da sojojin da ke kula da yankin. Hakazalika na sanar da Sarkin Dansadau amma babu abinda aka yi," Yusuf ya sanar da Premium Times.

Ya ce jami'an tsaro sun isa yankin ne bayan 'yan bindigar sun tsere. Ya ce daga bisani dai jami'an tsaron sun taya jana'izar mamatan.

Yusuf da sauran mazauna yankin sun tabbatar da cewa mutum 23 ne aka birne tsakanin Asabar da Lahadi bayan harin.

KU KARANTA KUMA: Rikicin APC: Shugaban majalisa, Ahmed Lawan ya saka baki

A lokacin da aka tuntubi kwamishinan tsaro, Dauran, ya ce gwamnati ta tura jami'an tsaro yankin don duba yadda 'yan bindiga ke shiga daga jihohin Katsina da Kaduna masu makwabtaka da su.

Kwamishinan bai musanta zargin gwamnati da ake yi da samun rahoton za a kai harin ba amma ta ki yin komai a kai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel