Abu kamar wasa: Wani Matashi ya auri Budurwar da ya hadu da ita a Twitter
- Wata Baiwar Allah ta bayyana yadda ta hadu da Angonta a shafin Twitter a shekarar 2019
- @aysha_yayari ta fito da hotunan aurenta da Saurayin da su ka hadu a kafar sada zumunta
- Ba wannan ba ne karon farko da dandalin sada zumuntan zamani su ka hada aure a kasar
Wata Baiwar Allah mai suna Nana Aysha Yayari, ta bada labarin yadda haduwarta da wani Matashi a kan shafin sada zumunta na zamani ya kai ga sanadiyyar aurensu.
Soyayyar wannan Matasa ya fara ne kamar wasa a shafin Twitter, inda Malam Hassan Muazu ya lallaba a asirce ya aika mata da sakon sirri watanni kimanin 18 da su ka wuce.
Yanzu labarin wadannan Masoya ya zagaye gari bayan Aysha Yayari ta bayyana yadda Twitter ya hada ta da Masoyinta. A karshen makon jiya lamarin ya kai an daura masu aure.
A ranar Asabar 20 ga watan Yuni, 2020 Hassan Muazu ya auri Sahibarsa Aysha Yayari. Amaryar ta ce sun fara haduwa ne shekara daya da rabi, yanzu ga shi sun zama mata da miji.
KU KARANTA: Aure ya sukurkuce bayan an gano Miji ya na da wata Mata
“Watanni kimanin 18 da su ka wuce, wannan Matashi ya aiko mani sakon DM da karfe 7:00 na safiyar wata ranar Asabar (shin, wa ke turawa Budurwa sako da sassafe haka a ranakun hutu)
Amarya Nana Aysha, ta kara da cewa: “Yau ga shi ina auren wannan mutumi, kuma babu abin da ya fi hakan farin ciki.” A karshe ta kara da godewa Ubangiji; Ta ce: “Alhamdulillah❤️."
Kusan mutane 30, 000 su ka nuna sha’awar wannan labari a Twitter, su ka rika aikawa Ma’aurantan sakonnin taya murna da Ubangiji ya ba su zaman lafiya da zuri’a mai albarka.
Muazu ya nuna cewa tun farkon da ya fara zura idanunsa a kan kyakkyawar amaryar ta sa a yau, ya ke tunaninta, a karshe ya yi nasarar yin caraf da ita a matsayin mai dakinsa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng