John Oyegun: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ceci Jam’iyyar APC tun yanzu

John Oyegun: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ceci Jam’iyyar APC tun yanzu

Wani tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Cif John Odigie-Oyegun ya yi kira ga majalisar zartarwa ta NEC ta jam’iyyar mai mulki, da ta yi maza ta kira taro domin a shirya sabon zabe.

A wani jawabi da John Odigie-Oyegun ya fitar mai taken “kafin lokaci ya kure”, ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar APC musamman shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni da su daina ‘abin kunya.’

Jaridar Daily Trust ta ce Odigie-Oyegun ya nemi majalisar NEC ta kafa kwamitin rikon kwarya da za su shirya zabe na musamman.

“An kafa APC ne da gumin ‘Yan Najeriya; yara da tsofaffi da ba za a iya bayyana adadinsu ba, da su sadaukar da rayuwarsu domin ganin siyasa ta cigaba. Ba za mu bari wannan sadaukar da kai da aka yi, ya tafi a banza ba.”

“Lokacin da za ayi wani abu shi ne yanzu, kafin lokaci ya kure sosai.” Inji Oyegun.

Dattijon ya ke cewa a lokacin da kasashe su ka cigaba ta bangaren siyasa, har yanzu abubuwa ba su sake zani a Najeriya ba tun da APC ta karbi mulki daga hannun PDP.

KU KARANTA: Sabon Shugaban Jam’iyya ya fadi hanyar da za a sasanta rikicin APC

John Oyegun: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ceci Jam’iyyar APC tun yanzu
John Oyegun
Asali: UGC

“A matsayina na tsohon shugaban jam’iyyar APC, ina alfahari da nasarorin gwamnatinmu a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari.”

Duk da haka Oyegun, ya na jin tsoron cewa ba a raba siyasa da kokarin da gwamnati ta yi a mulki. Oyegun ya ke cewa: “Tarihinmu na baya-bayan nan zai gaskata wannan magana.”

"A yau ana tuna Gwamnatin sojan Ibrahim Babangida ne da (soke zaben) 12 ga watan Yunin 1993 da abin da ya biyo baya.” Oyegun ya ce APC za ta wargaje idan ba a samu hadin-kai ba.

Ya ce: “A watannin baya mun ga yadda jam’iyyar (APC) ta yi fatali da manufofinta na tsabtar siyasa tare da yin fatali da duk wasu dokokin siyasa ta yadda za a iya yi wa wadanda su ka yi wa jama’a alkawarin kawo canji kallon yaudara da riddar siyasa.”

Cif Oyegun ya yi tir da yadda abubuwa su ke tafiya a yau. Ya ce: “Dole mu tuna da nasararmu a zaben 2015 da mika mana mulki da aka yi.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel