Rikicin APC: Gwamnoni 13 sun goyi bayan NWC, 7 na sukarsu

Rikicin APC: Gwamnoni 13 sun goyi bayan NWC, 7 na sukarsu

Rikicin cikin gida na jam'iyyar APC ya raba kan gwamnoni zuwa gida biyu. Yayin da gwamnoni 13 ke goyon bayan kwamitin gudanar da ayyuka karkashin jagorancin Abiola Ajimobi, wasu gwamnoni bakwai na sukar hakan.

Bakwai daga cikin gwamonin wadanda suka kira kansu da "masu gyara" sun kosa don kwace tafiyar da jam'iyyar kafin zuwan zaben 2023.

Gwamnonin 13 sun kira bakwai din da "masu mafarki da rana tsaka".

Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a jam'iyyar a halin yanzu suna bukata tare da rokon zaman lafiya.

Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, John Odigie-Oyegun da mataimakin sakataren jam'iyyar na kasa, Yekini Nabena a jiya sun yi kira da kawo karshen rikicin.

Tsohon mataimakin sakataren jam'iyyar, Victor Giadom na kokarin kwace shugabancin jam'iyyar.

Rikicin APC: Gwamnoni 13 sun goyi bayan NWC, 7 na sukarsu
Rikicin APC: Gwamnoni 13 sun goyi bayan NWC, 7 na sukarsu Hoto: The Source Magazine
Asali: UGC

A jiya Oshiomhole ya ce Giadom ya shirya cutarwa kamar yadda bangarenshi ya aikata a Ribas.

Nabena ya nuna irin wannan zargi da kushe game da Giadom.

Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, gwamnoni 13 da ke goyon bayan NWC ta Ajimobi tana ganin hannun jam'iyyar PDP a cikin rikicin sannan ta dauki alkawarin shawo kan al'amarin.

Amma kuma, sauran gwamnoni bakwai din APC da basu goyon bayan Ajimobi basu damu da shugabancin jam'iyyar ba.

An gano cewa wasu daga cikin ministocin Buhari na assasa wutar al'amarin.

Majiyoyi da dama sun ce manufar wannan sashin na jam'iyyar shine gyara ta kafin zaben 2023.

KU KARANTA KUMA: Bauchi: 'Yan sanda sun kama matashi da ya lalata kaninsa

An gano cewa Gwamna Zulum tare da wasu shugabannin jam'iyyar ne suka bankado shirin yayyaga bayanin taron da APC ta yankin arewa maso gabas tayi a Gombe a ranar Asabar.

Yunkurin yaga bayanan taron na nufin bude hanyar sabon rikici a jam'iyyar bayan wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bukaci Giadom ya zama mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa.

Mataimakin shugaban jam'iyyar na arewa maso gabas, Kwamared Mustapha Salisu, wanda ake zargi da mika bukatar a gaban kotu, ya ce bai taba mika hakan ga kotu ba.

Ya kara da cewa bai bukaci wani ya mika wannan bukatar ba a madadinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel