Eta ya fadi yadda rigimar shugabancin APC za ta zama tarihi da zaman NEC
Idan har ana so a ga karshen rigimar cikin gidan jam’iyyar APC na din-din-din, dole majalisar koli ta NEC ta jam’iyyar ta kira taro na musamman domin a zauna a nemi mafita mai dorewa.
Prince Hilliard Eta ya bayyana wannan bayan ya dare kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa a madadin sanata Abiola Ajimobi wanda har yanzu ya na kwance ya na fama da rashin lafiya.
Mista Prince Hilliard Eta ya ce: “Ita (NEC) ta na iya kawo karshen duk wadannan matsalolin da ake samu, idan har ana neman mafita da za ta wanye, ya zama dole mu kira taron NEC.”
Jaridar Daily Trust ta ce jam’iyyar APC ta shirya gudanar da taron NEC a ranar 17 ga watan Maris, amma daga baya aka dakatar da wannan taro bayan ganawar gwamnoni da shugaban kasa.
A cewar Prince Hilliard Eta, an dakatar da wannan zama na NEC ne saboda annobar cutar COVID-19 da ake fama da ita, Eta ya ce babu wanda ya ke jin tsoron majalisar NEC ta zauna.
Hilliard Eta ya ke cewa: “Ina tunanin abin da ya hana NEC zama a cikin ‘yan kwanakin bayan nan ita ce annobar cutar COVID-19, wanda ta hana kayyadadun mutane su zauna a wuri guda."
KU KARANTA: Tirka-tirkar shugabancin APC ta jefa Bola Tinubu a tsaka mai-wuya
"Ku sani cewa mu na da mutane fiye da 120 a majalisar NEC.” inji sa.
Sabon shugaban rikon kwaryar jam’iyyar ya yi alkawarin hada-kai da majalisar NEC a madadin NWC domin a shawo kan duk matsalolin cikin gidan da su ka bijirowa jam’iyyar APC a yau.
“Na san cewa zafin da abubuwa su ka yi a APC ya kai dole a samu irin wannan zama na musamman a cikin jam’iyya, a wuri na wannan shi ne muhimmin abin da ya kamata in maida hankali a kai.”
“Abu na biyu shi ne a karkare batun zaben tsaida ‘dan takarar jam’iyya a jihohin Edo, idan kuma ina nan har nan gaba, da (zaben) Ondo da wasu zabuka da za ayi domin cike gurabe a majalisa.”
A game da dokar da gwamnatin Godwin Obaseki ta kawo a jihar Edo wanda za ta haramtawa APC gudanar da zaben kato-bayan-kato, Eta ya ce mutane 20 za su fita su kada kuri’arsu a lokaci guda.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng