Oshinwo: Ambode, Abike-Dabiri, Ashafa, za su yi harin Majalisar Dattawa

Oshinwo: Ambode, Abike-Dabiri, Ashafa, za su yi harin Majalisar Dattawa

Rahotanni daga jaridar Daily Trust sun shaida mana cewa manyan ‘yan siyasan jihar Legas sun soma hangen kujerar Sanatan Legas ta gabas jim kadan bayan mutuwar Bayo Oshinowo.

A ranar Litinin ne Sanata Bayo Oshinowo ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya, ana zargin cewa cutar Coronavirus ce ta kashe ‘dan majalisar dattawan kasar mai shekaru 64 a Duniya.

Sunaye sun fara yawo na wadanda ake sa ran za su nemi kujerar ‘dan majalisar. A jam’iyyar APC akwai akalla fitattun mutane biyar da ake tunanin za a gwabza da su wajen takarar kujerar.

Ga wasu daga cikin wadanda ake hasashen za su nemi takara a zaben cike gurbin da za ayi nan gaba:

Dr. Tola Kasali ya na cikin wadanda su ka yi fice a jam’iyyar APC daga wannan yanki. Kasali tsohon kwamishina ne a gwamnatin Bola Tinubu, kuma ya na cikin hadimai a gwamnatin Raji Fashola.

KU KARANTA: Sanata Ajimobi ya na nan da ransa bai mutu ba

Oshinwo: Ambode, Abike-Dabiri, Ashafa, za su yi harin Majalisar Dattawa
Marigayi Sanata Oshinwo
Asali: UGC

Abike Erewa Dabiri ta taba zuwa majalisar wakilan tarayya kuma har yanzu ta na cikin matan da jam’iyyar APC ta ke ji da ita. Kafin yanzu ta zama mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara.

Masu hasashe su na ganin watakila Sanata Gbenga Bareehu Ashafa ya sake neman komawa kujerar da ya bari. Kafin yanzu ya rike mukamai da dama a gwamnatin Legas kuma ya na cikin jagororin APC.

Tsohon gwamna Akinwumi Ambode ya na cikin wadanda za su iya samun tikitin Sanata mai wakiltar gabashin Legas. Ambode ya rasa kujerarsa tun bayan da APC ta hana shi tikitin neman tazarce.

A PDP kuwa, rahoto ya nuna akwai yiwuwar wannan karo jam’iyyar ta tsaida Babatunde Gbadamosi wanda ya nemi gwamna a bara. A 2019, Princess Abiodun Oyefusi ce ta rikewa PDP tuta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel