Tunbuke Oshiomhole ya dagwulawa Bola Tinubu lissafi a Jam’iyyar APC

Tunbuke Oshiomhole ya dagwulawa Bola Tinubu lissafi a Jam’iyyar APC

Dambarwar shugabancin da ake fama da shi a jam’iyyar APC ya na jefa gidan siyasar jagoran jam’iyya kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu cikin wani yanayi.

Jaridar Daily Trust ta samu labari daga majiya mai karfi cewa dakatar da Adams Oshiomhole da kotu ta yi daga kujerar shugaban jam’iyya na kasa ya jefa siyasar Bola Ahmed Tinubu a matsala.

Yayin da bangororin jam’iyyar APC mai mulki su ka fara hangen zaben 2023, ana tunanin Bola Ahmed Tinubu ya na tare da Adams Oshiomhole wanda dakatar da shi ya jefa APC a cikin rudani.

A halin yanzu mutane da-dama sun fito su na gabatar da kansu a matsayin wadanda za su rike jam’iyyar APC. Daga cikinsu akwai Victor Giadom da tsohon gwamna Sanata Abiola Ajimobi.

Victor Giadom ya na da goyon bayan wasu gwamnoni da masu rike da mukamai a APC irinsu Rotimi Amaechi da Nasir El-Rufai, shi kuma Abiola Ajimobi ya na tare da mutanen Bola Tinubu.

Wani na-kusa da Bola Tinubu ya shaidawa jaridar cewa: “A karshe mun ji dadi a gidan Asiwaju inda aka tabbatar da Abiola Ajimobi (a matsayin shugaban jam’iyya na rikon kwarya.)”

KU KARANTA: Abin da ya sa ake rigima a Jam'iyyar APC - Ayo Fayose

Tunbuke Oshiomhole ya dagwulawa Bola Tinubu lissafi a Jam’iyyar APC
Adams Oshiomhole Hoto: APC
Asali: Depositphotos

Da aka tuntubi Mai magana da yawun bakin jam’iyyar APC a Legas, Seye Oladejo, ya bayyana cewa su na goyon bayan matakin da majalisar NWC ta dauka na tsaida sanata Ajimobi.

“Mutane za su so su jefa Asiwaju cikin rikicin jam’iyyar, saboda shi (Asiwaju) ya zama wani tubali a siyasar Najeriya. Bari ma ta wannan, APC ta Legas ta na tare da NWC.” Inji Seye Oladejo.

Duk da wannan, Giadom ya na kalubalantar matsayar Abokan aikinsa, inda ya hakikance a kan cewa shi ne shugaban jam’iyya na rikon kwarya domin tun tuni an dakatar da Oshiomhole.

Jihohin Yarbawa biyar daga cikin shida da ake da su, sun bada cikakken goyon bayansu ga Ajimobi. Jihar da ta kawowa uwar jam’iyya matsala ita ce Ekiti wanda ke rike da kujerar a baya.

A na sa bangaren Adams Oshiomhole ya yi kira ga Gaidom ya yi wa uwar jam’iyya biyayya. A daidai lokacin da Ajimobi ya ke jinya, Prince Hilliard Eta ne ya ke rike kujerar a matsayinsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel