Kotu ta tsawaitawa Gwamnatin Edo umarnin hana cafke Adams Oshiomhole

Kotu ta tsawaitawa Gwamnatin Edo umarnin hana cafke Adams Oshiomhole

A yau ranar Laraba ne wani babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ya tsawaita umarnin haramtawa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki cafke tsohon gwamna Adams Oshiomhole.

Alkali Ahmed Mohammed ya bada umarnin a dakatar da maganar kama Adams Oshiomhole bisa zargin da wani kwamitin bincike ya ke yi masa na cewa ya taba dukiyar gwamnatin jihar Edo.

Mai shari’a Ahmed Mohammed ya nemi duk masu hannu da ta-cewa a yunkurin kama tsohon gwamnan kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, da su jira sai zuwa karshen watan Yunin nan.

A ranar 29 ga watan Yuni ne kotu za ta zauna domin sauraron karar da Adams Oshiomhole ya shigar inda ya nemi a kare hakkinsa a matsayinsa na Bil Adama daga cin mutuncin gwamnati.

Wadanda alkalin ya takawa burki da wannan gajeren hukunci da ya yanke a zaman yau su ne: gwamnatin jihar Edo, kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin Godwin Obaseki.

KU KARANTA: Tsohon Gwamnan Gombe ya na goyon bayan tazarcen Obaseki

Kotu tsawaitawa Gwamnatin Edo umarnin hana cafke Adams Oshiomhole
Gwamna Obaseki da Shugaban kasa da COS Hoto: Twitter
Asali: Facebook

Sauran wadanda shari’ar ta shafa sun hada da shugaban kwamitin da ya binciki gwamnatin Adams Oshiomhole watau Alkali J. Oyomire, da sufeta janar na ‘Yan sanda da hukumar DSS.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa a shari’ar da aka yi a ranar 1 ga watan Yuni, an dakatar da Gwamna Godwin Obaseki da jami’an tsaro cafke Oshiomhole bisa zargin binciken da aka yi.

Kwamred Adams Oshiomhole ya yi mulki a jihar Edo tsakanin 2008 zuwa 2016. Bayan ya sauka daga karagar mulki ne Godwin Obaseki ya gaji kujerarsa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

A binciken da J. Oyomire ya gudanar, ya bankado cewa gwamnatin Adams Oshiomhole ta na da laifin satar dukiya daga baitul malin jihar Edo da kuma yi wa tattalin arzikin jihar zagon-kasa.

Da wannan hukunci da Alkali ya yanke dazu, babu wanda zai iya sa hannu ya kama tsohon gwamnan sai an karkare sauraron shari’a. Oshiomhole ya kai kara ne ta hannun Ehiogie Idahosa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng