Katsina: 'Yan bindiga sun halaka mutum 5 a kauyen Dan Ali

Katsina: 'Yan bindiga sun halaka mutum 5 a kauyen Dan Ali

Arangama tsakanin ‘yan sa kai da ‘yan bindiga a Dajin Gwamna da ke kauyen Dan Ali na karamar hukumar Danmusa a jihar Katsaina ya kawo rashin rayuka 5, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Biyu daga cikin mamatan masu suna Abdullahi Lawal wanda aka fi sani da Kirgi da Isiya Kanawa duk ‘yan sa kai ne da ke kauyen Dan Ali.

An gano gawawwakinsu a halin yanzu amma ba a birnesu ba saboda ‘yan bindigar sun hana damar yi musu jana’iza.

Rikicin ya fara ne a washegarin da aka kashe dagacin kauyen Mazoji da ke da kusanci da su. Daga nan ne ‘yan sa kan suka hadu a kauyen Dan Ali sannan suka yanke hukuncin shiga dajin don daukar fansa.

Katsina: 'Yan bindiga sun halaka mutum 5 a kauyen Dan Ali
Katsina: 'Yan bindiga sun halaka mutum 5 a kauyen Dan Ali Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Bayan arangamar, shugaban kungiyar ‘yan bindigar da ke yankin mai suna MaiNero ya bada umarnin harar kauyen Dan Ali, lamarin da yasa wasu mazauna kauyen suka fara gudun hijira.

An gano cewa an nema sasanci tsakanin ‘yan bindigar da mazauna kauyen bayan hana daukar gawawwakin da suka yi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Majalisar jihar Niger ta yi wa gwamnan jihar kirar gaggawa

“Muna fatan zuwa daren yau za mu birne su saboda ‘yan bindigar sun fara nuna mana sassauci,” wata majiya tace.

Rundunar ’yan sandan jihar har yanzu basu amsa tambayoyin da aka musu ba.

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da mataimakin shugaban karamar hukumar Shelleng na jihar Adamawa.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar sun isa gidan Kama Lazarus Bakta sannan suka yi awon gaba da shi.

Masu garkuwa da mutanen sun isa gidan a sa'o'in farko na ranar Talata inda suka dinga harbi a iska kafin su samu shiga gidan.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce 'yan sanda da mafarauta tuni suka fara bin sahun masu garkuwa da mutanen don cetosa.

Mazauna yankin da suka tattauna da Daily Trust sun koka da yawaitar sace manyan mutane da ake yi a yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel