Na samo takarduna na makaranta da suka bata - Gwamna Obaseki

Na samo takarduna na makaranta da suka bata - Gwamna Obaseki

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya sanar da cewa ya samu takardunsa na makaranta da suka bata.

Shugaban kwamitin tantance 'yan takarar gwamnan jihar Edo a jam'iyyar APC, Farfesa Jonathan Ayuba, shi ne ya bayar da sanarwar haramtawa Gwamna Obaseki tsayawa takara tun gabanin zaben fidda gwani.

Farfesa Ayuba ya bayyana cewa an haramta wa Obaseki tsayawa takara ne sakamakon matsalar da aka gano akwai a tattare da takardunsa na makaranta, kasancewar gwamnan ya gaza gabatar da takardu na asali sai na kwafi.

Amma da yake magana da manema labarai jim kadan bayan kammala ganawarsa da shugaba Buhari a fadar gwamnati, Obaseki ya bayyana cewa ya samo asalin takardunsa na karatu da ya manta inda ya ajiyesu shekara da shekaru.

Da ya ke mayar da martani a kan cewa akwai wasu alamomin tambaya a tattare da takardunsa na karatu, Obaseki ya ce: "babu yadda za a yi mutumin da bai halacci makaranta ba, bashi da wata takardar shaidar karatu, ya fahimci cewa akwai wata matsala a jikin takardun kammala makaranta.

Na samo takarduna na makaranta da suka bata - Gwamna Obaseki
Obaseki, Oshiomhole da Shaibu
Asali: UGC

"Mene ne matsalar da ke tattare da takarduna? Babu wata matsala a tattare da takarduna. Magana ce tun shekarar 2016, lokacin da na fara tsayawa takara, amma na kasa nemo takarduna da na manta inda na ajiyesu saboda na shafe fiye da shekaru 20 ban yi amfani dasu ba.

"Na je na yi takardar rantsuwa a kotu a kan cewa na rasa takarduna na karatu tunda banga asalin takarduna ba da na ajiye.

DUBA WANNAN: Shekau ya saki sabon bidiyo, ya nemi 'yan bindiga su hada kai da Boko Haram

"Daga baya kuma na ga dukkan takarduna, wadanda yanzu haka suna tare da ni. Ni ban fahimci wacce matsala suke nufin akwai a tattare da takarduna ba

"Watakila suna magana a kan yadda aka rubuta sunana a kan takardar shaidar kammala bautar kasa, sun tambayeni kuma na yi musu bayanin cewa haka hukumar NYSC ta ke rubuta sunaye a jikin takardar shaidar kammala bautar kasa.

"Idan a wurinsu hakan na nufin matsala, to sai dai na jajantawa Najeriya a kan rashin samun mutane masu ilimi a matsayin shugabannin jam'iyyar gwamnati mai ci

"Shi dama yana neman duk wani uzuri da zai yi amfani da shi domin haramta min takara, sai gashi jam'iyya ta bashi damar yin yadda yake so ba tare da la'akari da hatsarin da ke tattare da yin haka a tsarin dimokradiyya ba

"Dole ba za a taba ganin daidai ba duk lokacin da aka bawa mutane marasa ilimi da tarbiya jagoranci, ba za a samu adalci ba, ta haka zasu lalata duk wani abu mai kyau da tsari saboda son rai irin nasu," a cewar Obaseki.

Tuni Obaseki da mataimakinsa, Philiph Shaibu, suka sanar da ficewa daga jam'iyyar APC a ranar Talata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel