Mutane 79 za su rika taimakawa Hon. Shehu Nicholas Garba a Majalisa

Mutane 79 za su rika taimakawa Hon. Shehu Nicholas Garba a Majalisa

Shugaban kwamitin yaki da cin hanci da rashawa a majalisar wakilan tarayya, Shehu Nicholas Garba ya nada mukarrabai 79 da za su taimaka masa wajen sauke nauyin da ke kansa.

Honarabul Shehu Nicholas Garba ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya fitar a ranar 16 ga watan Yuni, 2020 ta bakin mai taimaka masa wajen harkokin yada labarai, Mista Mock S. Kure.

Mock Kure ya shaidawa manema labarai cewa mai gidansa ya taya wadanda ya zaba a matsayin Hadiman na sa murnar wannan romo na damukaradiyya da za su dandana a majalisar kasar.

A cewar Kure, ‘dan majalisar mai wakiltar mazabar Jama’a da Sanga ya bayyana wannan nadin mukamai da ya yi a matsayin abin da ba a taba yi ba tun da aka dawo mulkin farar hula.

‘Dan majalisar ya yi kira ga sababbin hadiman su taimaka wajen shiga harkar yakin neman zabe, sannan kuma su tasa wadanda aka zaba a majalisa a gaba domin ganin sun sauke nauyinsu.

KU KARANTA: Gwamna Obaseki ya fice daga Jam'iyyar APC bayan haramta masa neman tikiti

Mutane 79 za su rika taimakawa Hon. Shehu Nicholas Garba a Majalisa
Shugaban Majalisar Wakilai Hoto: Majalisa
Asali: Facebook

Shehu Nicholas Garba ya yi alkawarin zai goyi bayan ganin an yi wa tsarin zabe garambawul a majalisa ta yadda za a koma amfani da na’ura mai kwakwalwa wajen kada kuri’a a zabe.

Hadiman da aka dauka aiki sun fito ne daga mazabu 23 daga cikin kananan hukumomin Jama’a da Sanga. Mukarraban za su taimakawa ‘dan majalisar wajen harkar siyasa da tsare-tsare.

Daga cikin aikin da masu bada shawarar za su yi, akwai taimakawa a bangaren kawo kudirori a majalisa, jawo hankalin mata da kananan yara, da kuma kula da da dattawa, da yada labarai.

Garba ya ke cewa ya yi amfani da kwarewar aiki da biyayya ga jam’iyyar PDP wajen zakulo wadannan mukarrabai. Ya yi kira ga wadanda aka zaba su yi aikin da zai taimakawa al’umma.

A cikin wadannan hadimai da aka dauka, akwai wadanda su ka wakilci masu fama da nakasa. A dokar kasa, ‘dan majalisar ya na da hurumin daukar masu bada shawara biyar ne kacal.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel