Badakala: Ana zargin John Ohireime Asein da aika-aika a NCC
Ana zargin Darekta Janar na hukumar ‘Nigeria Copyright Commission’ da ke kare hakkin kirkire-kirkire a Najeriya, John Ohireime Asein da aikata laifuffukan da su ka sabawa dokar aiki.
Wani bincike da Economic Confidential ta yi ya nuna cewa John Ohireime Asein shi ne shugaban kamfanin REPRONIG wanda hukumar da ya ke jagoranta ta kasa ta ke lura da shi, wanda hakan ya sabawa dokar aikin gwamnati da tsarin mulki.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa akwai korafe-korafe a kan Mista John Ohireime Asein daga kungiyoyi da-dama, amma a karshe hukumomin da ke binciken yaki da cin hanci da rashawa sun yi watsi da wadannan kuka da jama’a su ke yi.
Wata kungiya ta manyan ma’aikatan hukumar ta rubuta takarda inda ta ja hankalin gwamnati a game da yadda John Asein ya ke cigaba da rike kujerar shugaban kamfanin REPRONIG a daidai lokacin da ya ke da mukamin gwamnati.
John Ohireime Asein ya karbi albashi biyu a ma’aikatun da ya ke aiki, wannan ya ci-karo da tsarin aiki a Najeriya. Misali binciken ya nuna cewa a cikin watan Mayun 2019, John Ohireime Asein ya karbi N366,000.00 da N377,000.00.
KU KARANTA: WTO: Najeriya ta samu kwarin gwiwa bayan samun goyon bayan Benin
A ranar 11 ga watan Yuni, 2019, an biya John Asein N150,000.00 ta hannun wani ma’aikacin kamfaninsa. A cikin watan Yulin na bara, Asein ya karbi wasu kudi a dunkule: N359,000.00, N292,000.00 da N304,000.00
Haka zalika an biya irin wannan kudi a watannin Agusta, Satumba da Oktoba. Abin da ya shiga hannu wanda ake zargin ta bayan fage ya kusan kai Naira miliyan.
Bayan haka shugaban hukumar kasar ya boyewa ma’aikatar kudi da masu bincike labarin wasu kudi da ya samu daga gwamnatin kasar Faransa.
Bugu-da-kari Darekta Janar din ba ya tuntubar majalisar da ke kula da hukumarsa kafin ya yi amfani da kudin da su ka zarce N5m. A matsayinsa na Lauya, ya kamata ace ya san da wannan doka.
Da Economic Confidential ta tuntubi Asein domin ya wanke kansa daga zargin, ya bayyana cewa ba zai tanka ba domin maganar ta na hannun ma’aikatar shari’a, kuma an tuhumesa a baya.
Aikin da Asein ya ke yi a kamfanin REPRONIG zai jefa hukumar tarayya da ke kare hakkin kirkire-kirkire cikin tsaka mai-wuya, don haka ne dokar kasa ta haramta aiki a wuraren biyu a lokaci guda.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng