Tsaro: APC ta yi wa PDP raddi a kan bukatar murabus din Masari

Tsaro: APC ta yi wa PDP raddi a kan bukatar murabus din Masari

- An yi musayar yawu tsakanin jam' iyyun APC da PDP a jihar Katsina kan neman Gwamna Aminu Masari ya yi murabus

- Jam'iyyar PDP dai ta bukaci Masari ya sauka daga shugabancin jihar, cewa ya gaza wajen tsaron al'ummansa

- Hakan ya biyo bayan hakuri da gwamnan ya bayar, inda ya jajanta yadda ya kasa kawo karshen miyagun ayyukan 'yan bindiga a jiharsa

Jam'iyyun APC da PDP sun yi musayar yawu kan kira ga gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari da yayi murabus sakamakon ci gaban ayyukan barnar 'yan bindiga a jihar.

A tattaunawa da aka yi da gwamnan har kashi biyu, an ji yana jajanta yadda ya kasa kawo karshen miyagun ayyukan 'yan bindiga a jiharsa.

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Katsina, Salisu Majigiri, a wata tattaunawa da aka yi da shi ya ce abinda Masari ya bayyana ya nuna gazawar jam'iyyar APC a jihar tare da zama koma baya ga ci gaban da PDP ta kawo jihar tun daga 1999.

Tsaro: APC ta yi wa PDP raddi a kan bukatar murabus din Masari
Tsaro: APC ta yi wa PDP raddi a kan bukatar murabus din Masari Hot: The Nation
Asali: Facebook

Kamar yadda yace, gwamnan ya mika dukkan yardarsa ga 'yan bindiga amma daga baya ya sanar da cewa sun ci amanarsa.

Amma da aka tuntubi shugaban jam'iyyar APC ta jihar, Bala Musawa, ya ce PDP na amfani da wannan damar ne wurin suka. Gwamnan na nuna tsantsar gaskiyarsa ne wanda hakan ne ya dace da shugaba nagari.

Musawa yace gwamnan ya yi niyyar sasantawa da 'yan bindigar ne da zuciya daga kuma dukkan malaman addinan jihar da masu ruwa da tsaki sun goyi bayan wannan ci gaban, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Musawa yace babu adalci idan aka gwada mulkin shekaru 16 na PDP da shekaru 5 na APC a jihar.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Yaki da korona na hannunku - El-Rufai ga jama'ar Kaduna

"APC ta zo ne a lokacin da aka gama wawure tattalin arziki sannan ga karin annobar da ta barke wacce ta dakusar da mulki."

A wani labarin kuma, mun ji cewa a kalla mutum 10 suka rasa rayukansu sakamakon harin 'yan bindiga a karamar hukumar Agatu da ke jihar Binuwai.

Daily Trust ta gano cewa a halin yanzu an samu gawawwaki 10 amma kuma wasu sun bace sakamakon harin.

Shugaban karamar hukumar Agatu, Usman Suleiman, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar Daily Trust ta waya, ya ce har yanzu babu wani cikakken bayani game da harin sassafen.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng