'Yan bindiga sun halaka 'yan sanda biyu a Neja
A ranar Juma'a ne 'yan bindiga suka harbe 'yan sanda biyu har lahira a kauyen Kusasu da ke yankin Erena na karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
An gano cewa 'yan sandan da suka hada da sifeta tare da kofur na tsaron wurin samar da wutar lantarki a Shiroro da ke kan hanyar kauyen Kauore da ke Birnin Gwari a jihar Kaduna.
'Yan sandan na aiki ne a ofishin 'yan sanda da ke Zumba kuma sun yi musayar wuta tsakanin su da 'yan bindigar.
Duk da 'yan sandan sun yi nasarar bai wa Injiniyoyin kariya, amma sun rasa rayukansu sakamakon raunikan da suka samu daga harbin bindiga.

Asali: UGC
Kamar yadda majiya mai karfi da ke kusa da kauyen ta sanar, an kashe daya daga cikin 'yan bindigar amma kuma an rasa 'yan sandan biyu saboda rashin yawansu.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Wasiu Abiodun ya ce 'yan sandan biyu sun bace sakamakon musayar wuta da suka yi da 'yan bindiga a kauyen Kusasu da ke karamar hukumar Shiroro.
Amma kuma yace an tura jami'an tsaro don ceto 'yan sandan. Ya bada tabbacin cewa za su damke 'yan bindigar babu jimawa.
KU KARANTA KUMA: Edo 2020: APC ta bukaci korar Obaseki da wasu mutum biyu
A wani labarin kuma, mun ji cewa a kalla mutum 10 suka rasa rayukansu sakamakon harin 'yan bindiga a karamar hukumar Agatu da ke jihar Binuwai.
Daily Trust ta gano cewa a halin yanzu an samu gawawwaki 10 amma kuma wasu sun bace sakamakon harin.
Shugaban karamar hukumar Agatu, Usman Suleiman, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar Daily Trust ta waya, ya ce har yanzu babu wani cikakken bayani game da harin sassafen.
Suleiman ya ce wurin karfe 7 na safe aka sanar da shi cewa mahara sun kai hari yankin kuma an gaggauta sanar da mataimaki na musamman a kan tsaro tare da rundunar Operation Whirl Stroke.
Ya jaddada cewa jami'an tsaron sun gaggauta kai dauki inda suka kama wasu matasa kuma sun samu gawawwaki 9.
Wani mazaunin yankin ya ce an samu bindiga kirar AK47 da harsasai 60 daga hannun shugaban 'yan bindigar wanda ya shiga hannun rundunar Operation Whirl Stroke.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng