Gwamna Aminu Masari ba zai sake wata takara bayan shekarar 2023 ba

Gwamna Aminu Masari ba zai sake wata takara bayan shekarar 2023 ba

Jaridar The Nation rahoto cewa gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya ce bayan ya bar ofis a 2023, ba zai sake neman wata kujerar siyasa a Najeriya ba.

Gwamnan ya bayyana cewa bai da wani burin takara bayan zaben 2023, a cewarsa daga wannan lokaci zai bar wa matasa harkar domin a cigaba da damawa da su.

Rt, Hon. Aminu Bello Masari ya ce zai rabu da siyasa ne domin zuwa 2023, ya kai shekara 73 a Duniya, don haka ya ke ganin zai fi kyau ya bar wa masu jini a jika.

Kamar yadda mu ka samu rahoto, mai girma gwamnan ya yi wannan bayani ne a gidan gwamnati.

Ya ce: “Na sanar da matsayina sarai, a yadda na tsara, ba ni da niyyar neman wata kujera bayan wannan. Ko a mafarki, ban taba tunanin zan shiga harkar siyasa ba.”

Gwamna Masari ya ce kaddara ce ta shigo da shi cikin siyasa.

KU KARANTA: Gwamna Aminu Masari ya haramta bara a Jihar Katsina

Gwamna Aminu Masari ba zai sake wata takara bayan shekarar 2023 ba
Gwamna Aminu Masari
Asali: Twitter

“Ban kutsa kai na cikin siyasa ba, kaddara ce, ban san cewa zama Kwamishina zai jefa ni siyasa ba, da na san da haka, da kila ban karbi tayin kujerar Kwamishina ba.”

Masari ya cigaba da cewa: “Ban tabbata cewa zan yi kyau da siyasa ba domin ni mutum ne wanda ya ke kan aiki ba wanda ya kware da shugabanci ba.”

“Burina shi ne in yi ritaya ba in nemi kujerar Sanata ba. Ba zan tafi majalisar dattawa ba. Idan Allah ya so, a 2023 zan cika shekara 73, zuwa wannan lokaci na gama.”

Aminu Masari ya rike kujerar shugaban majalisar wakilan tarayya a lokacin gwamnatin jam'iyyar PDP. Daga baya ya sauya-sheka, ya nemi mulki a APC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng