Manjo Janar Orho Obada ya rasu a Jihar Delta
Rahotanni daga jaridar Punch sun tabbatar da mutuwar Manjo Janar Orho Obada wanda ya rike mukamai da-dama a gwamnatin tarayya a Najeriya.
Kafin mutuwar Obada, ya rike kujerar kwamishina mai wakiltar jihar Delta a hukumar da ke da alhakin kasa albashi da alawus din ma’aikata a Najeriya.
An haifi Janar Obada ne a watan Afrilun 1939 a kasar Agbarho da ke garin Ughelli, jihar Delta. An sanarwa 'yan jarida mutuwarsa ne jiya Asabar a garin Warri.
Marigayin ya mutu ne ya na rike da kujerar majalisar amintattu ta babbar kungiyar kabilar Urhobo ta kasa. Obada ya bar Duniya ya na da shekaru 81.
Marigayi Obada ya yi karatun sakandare a garin Warri a 1958, daga nan ya tafi gidan soja inda ya samu horo a garin Tesha da Sandhurst a kasar Ghana da Ingila.
KU KARANTA: Dede Amaechi: 'Danuwan Ministan Shugaba Buhari ya mutu
Bayan ya dawo gida, Obada ya zama Dogarin Nnamdi Azikiwe daga 1964 zuwa 1966. A shekarar 1970 ne Obada ya taba rike kujerar shugaban hafsun sojin sama.
Bayan haka daga 1971 zuwa 1975, Obada ya zama shugaban makarantar sojojin sama da ke Kaduna. Haka zalika sojan ya rike GOC na sojojin shiyyar Enugu.
Manjo Janar Orho Obada ya rike kujerar ministan ayyuka a gwamnatin soji tsakanin shekarar 1976 zuwa 1977. Bayan ya ajiye kujerasa, ya yi ritaya daga gidan soja.
A lokacin da Orho Obada ya ke minista, Muhammadu Buhari ya na cikin gwamnati inda shi kuma ya ke ministan harkokin man fetur a gwamnatin Olusegun Obasanjo.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng