Damfara: Okorocha ya yi wa EFCC 'wankin babban bargo'

Damfara: Okorocha ya yi wa EFCC 'wankin babban bargo'

- Rochas Okorocha ya ce karyata batun cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa bata karbi N7.9 biliyan daga wurinsa ba

- Okorocha ya yi wannan martanin ne ga takardar da Imam Usman, shugaban EFCC na Fatakwal ya fitar a ranar Alhamis

- Ya kuma kalubalani hukumar da ta fito ta yi bayani dalla-dalla kan yadda ta karbi kudin, idan kuma akasin haka ne ta fito ta ba da hakuri

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya ce hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) bata karbi N7.9 biliyan daga wurinsa ba.

Okorocha ya yi wannan martanin ne sakamakon takardar da Imam Usman, shugaban EFCC na Fatakwal ya fitar a ranar Alhamis.

Ya ce hukumar ta mayar wa gwamnatin jihar N2.7 biliyan daga cikin N7.9 biliyan da ta kwato daga hannun Okorocha bayan ya wawure.

A takardar da ya fita a ranar Juma'a, Sam Onwuemeodo, mai magana da yawun Okorocha ya ce babu gaskiya a zancen da EFCC ta fitar a kan tsohon gwamnan.

Damfara: Okorocha ya yi wa EFCC 'wankin babban bargo'
Damfara: Okorocha ya yi wa EFCC 'wankin babban bargo' Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya bukaci hukumar da ta wallafa bayanai tare da sunayen mamallakan asusun bankin da suka samu kudin da suka kwace daga Okorocha.

"A matsayin EFCC na hukuma da kuma Usman Imam mai shugabantar ta a yankin, basu samu N7.9 biliyan ko wani kudi daga Rochas Okorocha ba," Onwuemeodo yace.

"Cike da musanta aukuwar lamarin, muna kalubalantar EFCC ko Imam da su wallafa bayanan yadda suka samu kudin.

"Muna girmama EFCC da jami'anta. Don haka muke bukatar su dauki musanta lamarin nan da muka yi da muhimmaci don 'yan Najeriya za su so sanin gaskiyar al'amarin.

KU KARANTA KUMA: Obaseki: Ana gayyato 'yan Bangar siyasa da makamai cikin jihar Edo

"Idan hukumar ta gano cewa ba gaskiya ta fada ba kuma ta bata wa tsohon gwamnan suna, muna so ta fito tayi abinda ya dace a kafafen yada labarai."

"Imam ya yi magana a kan kadarorin Okorocha da ta bankadao. Akwai bukatar Imam ya wallafa bayanai a kan kadarorin saboda Okorocha ya mallakesu kusan shekaru 20 da suka gabata kenan."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng