Rashin tsaro: Shugabannin NASS za su yi taro da Buhari

Rashin tsaro: Shugabannin NASS za su yi taro da Buhari

- Majalisar dattawan kasar nan ta yanke hukuncin zantawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Majalisar dattawan ta sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin da take tattaunawa a kan rashin tsaron da ya addabi kasar nan

- Dattawan sun yanke shawarar ne bayan da Sanata Abubakar Kyari da ke wakiltar jihar Borno ta tsakiya ya mika bukatar gaban majalisar

A sabon yunkuri na yakar rashin tsaro a fadin kasar nan, shugabannin majalisar dattawan Najeriya sun yanke hukuncin samun shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabannin tsaron kasar nan.

Majalisar karo ta tara a kasar nan ta cika shekara daya a mulki a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni. Ta yanke hukuncin kawo karshen kashe-kashen da ya yawaita a kauyukan wasu jihohi na kasar nan.

Legit.ng ta gano cewa, Sanata Abubakar Kyari mai wakiltar mazabar Borno ta Arewa ya mika bukatar yin taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari amma da shugabannin majalisar kadai.

A hukuncin dattawan, sun ce ya zama tilas shugabannin tsaron kasar nan su hanzarta daukar matakin kwace yankunan tafkin Chadi daga hannun 'yan ta'adda.

Rashin tsaro: Shugabannin NASS za su yi taro da Buhari
Rashin tsaro: Shugabannin NASS za su yi taro da Buhari Hoto: Loveworld
Asali: UGC

Idan za mu tuna, 'yan ta'addan Boko Haram sun halaka rayukan mutum 70 a ranar Talata, 9 ga watan Yuni a Borno.

Harin da aka kai a kauyen Faduma Koloram da ke karamar hukumar Gubio ta jihar Borno, ya dauki wurin sa'o'i 5 kamar yadda mazauna kauyen suka tabbatar.

A yayin zaman zauren majalisar na ranar Alhamis, dattawan sun bukacin NEMA da NEDC da ta gaggauta aika kayan rage radadi ga wadanda harin ya ritsa da su.

A wani labarin kuma, mun ji eewa rundunar sojin Operation Lafiya Dole ta kashe 'yan ta'addan Boko Haram tare da tarwatsa maboyarsu da ke Kacha Korle a dajin Sambisa na jihar Borno.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche, ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba.

Kamar yadda yace, sun yi wannan aikin ne a ranar 10 ga watan Yuni bayan bayanan sirrin da suka samu da ke nuna inda mayakan ta'addancin ke yin taro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel