Obaseki: Ana gayyato 'yan Bangar siyasa da makamai cikin jihar Edo

Obaseki: Ana gayyato 'yan Bangar siyasa da makamai cikin jihar Edo

- Gwamna Godwin Obaseki ya ce ya samu bayanan sirri da suka tabbatar da cewa wasu 'yan siyasa na gayyato 'yan daba da makamai cikin jihar don kawo tashin hankali a Edo

- Ya ce ana shigo da 'yan bindiga daga wasu jihohi zuwa jihar Edo gabannin zaben da za a yi

- Obaseki ya sha alwashin daukar mataki a kan duk wanda aka kama game da lamarin

Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo, ya ce ya samu bayanan sirri da suka tabbatar da cewa wasu 'yan siyasa na gayyato 'yan daba da makamai cikin jihar don kawo tashin hankali.

A wata takarda da ta fita a ranar Alhamis a babban birnin jihar, mai bada shawara na musamman ga gwamnan, Crusoe Osagie ya ce ana shigo da 'yan bindiga daga wasu jihohi zuwa jihar Edo.

Ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da ta kama duk wanda zai take doka.

Obaseki: Ana gayyato 'yan Bangar siyasa da makamai cikin jihar Edo
Obaseki: Ana gayyato 'yan Bangar siyasa da makamai cikin jihar Edo Hoto: Vanguard
Asali: UGC

"Gwamnatin jihar Edo ta samu bayanan sirri da ke tabbatar da cewa wasu 'yan siyasa na shigo da 'yan daba daga wasu jihohi ta hanyoyin ruwan jihar Edo da sauran iyakokin don tada zaune tsaye," yace.

"Muna sanar da jama'a tare da jan kunnensu a kan kiyaye sabbin fuskokin da za su iya shigowa cikinsu. Ana shawartar jama'a da su hanzarta sanar da jami'an tsaro duk wani mutum da basu yarda da shi ba don daukar mataki.

"Har ila yau, muna jan kunnen masu ajiye makamai da kokarin tada hankalai da su gujewa hakan. Don gwamnati ba za ta sassautawa kowa ba matukar ta kama shi da laifi. Za a damke mutum tare da mika shi gaban shari'a.

"Alhakin kare rayuka da dukiyoyi ya rataya a wuyan Gwamna Godwin Obaseki. Ba zai yi watsi da wannan hakkin ba saboda siyasa.

"A don haka ne ya saka hannu a kan haramta dukkan wani taron siyasa don gujewa yaduwar cutuka."

KU KARANTA KUMA: Korona: Muna cikin mawuyacin hali sosai, in ji Buhari

A yayin da aka saka ranar 19 ga watan Satumba don zaben jihar Edo, abubuwa na kara cabewa tsakanin Obaseki da Adams Oshiomhole duk a jam'iyyar APC.

Oshiomhole da bangarensa na goyon bayan Osagie Ize-Iyamu yayin da Obaseki ke son zarcewa.

Za a yi zaben fidda gwani a ranar 22 ga watan Yuni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel