Tantance 'yan takara: Babu alamun za ai min adalci -Gwamna Obaseki

Tantance 'yan takara: Babu alamun za ai min adalci -Gwamna Obaseki

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana shakkarsa a kan yiwuwar samun adalci a hannun uwar jam'iyyar APC a karkashin jagorancin Adams Oshiomhole.

Obaseki ya bayyana hakan ne jim kadan bayan fitowarsa daga dakin da ya shafe sa'a biyu ana tantance shi a hedikwatar jam'iyyar APC ta kasa da ke Abuja a ranar Laraba.

"Lokaci na karshe da na zo nan, na sanar da cewa ya kamata Oshiomhole ya tsame hannunsa daga dukkan harkokin tantance 'yan takara saboda ta hakane kawai za a samu tabbatuwar adalci.

"Amma, saboda mutunta tsarin jam'iyya, na halarci tantance 'yan takara kamar kowa.

"Tunda Oshiomhole ne alkalin da zai yanke hukunci a kan tantancewar, zan saurari sakamakon da zai fitar.

"Na basu dukkan bayanan da suke bukata; na kuma basu satifiket din jami'ar Ibadan da ake ta cece - kuce a kansa.

"Kamar yadda na fada, a matsayina na dan jam'iyya, na halarci matakin tantancewa, amma ban gamsu cewa za ai min adalci ba, saboda Adams Oshiomhole yana da bukata a kujerar gwamnan jihar Edo.

"Daga cikin tambayoyin da aka yi min akwai neman dalilin da yasa na bayar da umarnin dakatar da zaben kato bayan kato a fidda dan takarar gwamnan jihar Edo da uwar jam'iyya zata gudanar.

"Sun tambayeni; banga hakan a matsayin cin dunduniyar jam'iyya ba?, amma ni a ganina bai kamata a saka siyasa a maganar abinda ya shafi tsare lafiyar jama'ar jihar Edo ba," a cewar gwamna Obaseki.

Tantance 'yan takara: Babu alamun za ai min adalci -Gwamna Obaseki
Obaseki yayin da ya ziyaci Buhari da fom dinsa na takara
Asali: Twitter

A yayin da kwamitin zartarwa na uwar jam'iyyar APC ya aminta da salon zaben kato bayan kato, inda duk mai shaidar zama dan jam'iyya zai iya yin zaben dan takarar da yake so.

Magoya bayan Gwamna Godwin Obaseki ba su aminta da hakan ba. Sun fi son wakilan jam'iyyar su fito don yin zaben.

DUBA WANNAN: Dabiu'u 10 na yau da kullum da ke sukurkuta kwakwalwa

Baraka a kan yanayin zaben fidda gwanin ya kai ga zargin cewa bangaren shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, na tsananta yakin neman kada Obaseki.

'Yan takara biyar ne ke adawa da Obaseki, wadanda suka hada da: Pius Odubu, Osagie Ize-Iyamu, Chris Ogiemwonyi, Matthew Iduoriyekemwen da Osabo Obazee.

Shugaban jam'iyyar APC na Edo ta tsakiya, Chief Francis Inegbeniki, wanda yake na hannun daman Adams Oshiomhole, ya tattara laifuka 50 na Obaseki wadanda sun isa su hana gwamnan zarcewa.

Ya ce da yawa daga cikin 'yan jam'iyyar ba su amince da Obaseki da mataimakinsa ba saboda rashin jituwar da ke tsakaninsa da shugaban jam'iyyar tare da manyan jiga-jigan jam'iyyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel