‘Yan bindiga: Mutum 50 ake tsoron an kashe a karamar Hukumar Faskari

‘Yan bindiga: Mutum 50 ake tsoron an kashe a karamar Hukumar Faskari

- An sake kai wa mutanen karamar hukumar Faskari hari a Ranar Talata

- Ana zargin cewa mutane 50 ‘Yan bindigan su ka kashe ido na ganin ido

- Jami’an tsaro ba su kawo agaji ba sai bayan an gama hallaka Bayin Allah

Akalla mutum 50 ake tunanin cewa sun mutu bayan wani sabon hari da aka kai wani gari na Kadisau da ke cikin karamar hukumar Faskari, jihar Katsina.

Mun samu labari cewa ‘yan bindigan wadanda su ke dauke da manyan makamai sun shiga cikin wannan gari na Kadisau ne da kimanin karfe 4:30 na ranar Talata.

Channels TV ta ce wadannan miyagun mutane sun far ma garin ne a kan babura fiye da 100.

An kai wannan hari ne jim kadan bayan mutanen garin ‘Yantumaki da ke cikin karamar hukumar Danmusa sun fito sun yi zanga-zanga a dalilin matsalar rashin tsaron da su ke fama da shi.

Mutanen yankin ‘Yantumaki sun fito kan tituna su na nuna takaicin su ne bayan samun labarin an sace wani magidanci da kuma ‘diyarsa a cikin farkon makon nan.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai farmaki a Garin Yankara, sun kashe na kashewa

‘Yan bindiga sun matsawa mutanen yankin karamar hukumar Faskari da Sabuwa inda a ‘yan kwanakin nan an hallaka mutane da-dama a Kauyen Mairuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa miyagun sun duro garin ne da sakaliyar la’asar, sun yi abin da za su yi kafin jami’an tsaro su iya kawo wani dauki bayan rana ta fada.

‘Yan bindigan sun shafe fiye da sa’a guda su na ta’adi, sai kusan karfe 6:00 su ka fita daga garin.

Kawo yanzu, kakakin ‘yan sanda na jihar Katsina, SP Gambo Isah bai iya yi wa ‘yan jarida bayani game da wannan mummunan abu da ya sake faruwa a jihar ba.

Legit.ng Hausa ta yi magana da wata Baiwar Allah da ke karamar hukumar Faskari wanda ‘yan bindiga su ka addabe su, inda ta shaida mata cewa dole su bar gari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel