INEC ta amince da zaben kato-bayan-kato wajen fito da ‘Dan takarar APC a Jihar Edo

INEC ta amince da zaben kato-bayan-kato wajen fito da ‘Dan takarar APC a Jihar Edo

Jirgin yakin neman zaben Godwin Obaseki ya gamu da wani babban kalubale a kan hanya a ranar Talata, 9 ga watan Yuni, 2020, bayan hukumar zabe na INEC ta fadi yadda za a fito da ‘yan takara.

Hukumar zabe mai zaman kanta watau INEC ta amince da tsarin kato-bayan-kato wajen fito da ‘dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan da za a yi a jihar Edo.

Legit.ng Hausa za ta iya tunawa cewa wannan tsari da shugabannin jam’iyyar APC su ka kawo, ya bar baya da kura, inda musamman gwamna Godwin Obaseki da magoya bayansa su ke nuna rashin goyon bayansu.

Yayin da wasu na-kusa da gwamna Godwin Obaseki su ka huro wutan cewa manyan ‘yan jam’iyya ya kamata su fito da ‘dan takara, shugabannin APC na kasa sun dage a kan ayi zaben kato-bayan-kato.

A yayin da ake da ‘yan siyasa akalla shida da ke neman takarar gwamnan jihar Edo a karkashin APC, kowane bangare ya ki ja baya a kan bakarsa.

A wani jawabi da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta fitar, ta ce jam’iyyar APC ta zabi ta yi amfani da tsarin zaben kato-bayan-kato a jihar Edo.

KU KARANTA: Gwamna Obaseki ya ce Shugaban APC bai isa ya hana shi tazarce ba

INEC ta amince da zaben kato-bayan-kato wajen fito da ‘Dan takarar APC a Jihar Edo
Gwamna Obaseki da Shugaba Buhari Jihar Edo Hoto: APC
Asali: UGC

Mai magana da yawun bakin INEC, Festus Okoye, ya shaidawa Duniya wannan a jiya Talata.

Festus Okoye ya ce jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Edo, a na ta bangaren, ta zabi ayi amfani da ‘yar tinke ne wajen fito da wanda zai rike mata tuta a zabe mai zuwa.

A jawabin da INEC ta yi, ta ce jam’iyyu 15 cikin jam’iyyun siyasa 18 da za su shiga zaben gwamnan ne su ka nemi su yi zaben fitar da gwani wajen fito da ‘dan takararsu.

A game da abin da ya sa INEC ta yi na’am da matsayar da ka iya jefa gwamnan APC cikin matsala, Okoye ya bayyana cewa hukumar ta na aiki ne da matakin da shugabannin jam’iyya na kasa su ka zartar.

Daga cikin masu neman tikitin APC a zaben Satumban bana har da fasto Osagie Ize-Iyamu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel