Mun karbe dukiyar sama da Naira Biliyan 3 a iyakokin Arewa maso Yamma – Kwastam

Mun karbe dukiyar sama da Naira Biliyan 3 a iyakokin Arewa maso Yamma – Kwastam

Dakarun hukumar kwastam na Border Drill da ke jihar Katsina sun ce sun karbe wasu kaya da kudin shigowa da su ya kai Naira biliyan 3.2 daga watan Junairu zuwa yanzu.

Jami’an da ke yaki da fasa-kauri sun bayyana wannan ne ta bakin shugabansu na shiyyar Arewa maso yamma, Aliyu Mohammed, wanda ya ce sun kama kaya sau 801, sannan sun cafke mutane takwas da ke kokarin shigowa kasar ta barauniyar hanya a tsawon wannan lokaci.

Aliyu Mohammed ya yi wannan bayani ne a ranar Talata, 9 ga watan Yuni, 2020 a garin Kaduna.

Mohammed ya bayyana wasu daga cikin wadannan kaya da dakarun na NCS su ka yi nasarar cafkewa a hannun masu saba doka.

Daga cikin kayan da jami’an su ka gabatarwa ‘yan jarida a Kaduna akwai buhuna 1, 713 na yadin tufafi, da buhuna 5, 400 masu nauyin kilo 25 na shinkafa da aka boye a cikin buhunan kamfanonin gida.

KU KARANTA: Shugaban Hukumar Kwastam na kasa Hameed Ali ya sake aure

Mun karbe dukiyar sama da Naira Biliyan 3 a iyakokin Arewa maso Yamma – Kwastam
Jami'an Kwastam na Najeriya
Asali: UGC

Sauran kayan da aka kama sun hada da buhunan takin NPK 9,735 daga kasar waje da kuma lita miliyan 1.4 na man fetur da bakin mai.

Mohammed ya ke cewa bayan haka sun tare tulin tabar wiwi da gwanjon kayan sawa da wasu kwayoyin magani da allurai.

Jami’in na kwastam ya ce hada-kan da su ka yi da sauran hukumomin kasar ya taimaka wajen ba su wannan nasara na yin aikin su yadda ya kamata.

Haka zalika horaswar da aka yi wa jami’an na kwastam da kuma karin albashin da su ka samu, ya zaburar da su inji Aliyu Mohammed.

A cewarsa, ma’aikatan NCS su na bin matakan da hukumomin lafiya su ka kawo wajen aiki domin takaita yaduwar cutar COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel