EFCC: Babu hujjar da ke nuna da kudin jihar Kwara Saraki ya saye gidajensa – Kotu

EFCC: Babu hujjar da ke nuna da kudin jihar Kwara Saraki ya saye gidajensa – Kotu

A jiya ne Alkalin wani babban kotun tarayya da ke zama a Legas ya ki yin na’am da bukatar gwamnatin tarayya na karbe wasu kadarori na sanata Bukola Saraki har abada.

Hukumar EFCC ta bukaci kotu ta ba ta damar rike wadannan kadarori da tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya mallaka, amma kotu ta ki yarda.

A Oktoban 2019 ne hukumar EFCC ta samu damar soma rike wasu gidajen Bukola Saraki da ke kan titin McDonald a unguwar Ikoyi, a karamar hukumar Eti Osa a jihar Legas.

Daga baya lauyan EFCC ya roki kotu ta ba gwamnati damar maida wadannan gidaje a hannunta.

EFCC ta na zargin Saraki ya mallaki wadannan gidaje ne da dukiyar gwamnati.

EFCC ta ce a lokacin da Bukola Saraki ya ke gwamna a jihar Kwara, ya wawuri Naira biliyan 12 daga cikin asusun jihar, inda ya yi amfani da wannan kudi wajen fansar gidajen.

KU KARANTA: Alkaki ya yanke hukunci a karbe kudin 'Dan kasuwa a ba gwamnati

A cewar lauyan EFCC, tsohon gwamnan ya yi amfani da wani hadiminsa mai suna Abdul Adama wajen sayen gidajen, ya kuma ce an yi amfani ne da wasu manyan bankuna biyu.

Da ya ke yanke hukunci a ranar 8 ga watan Yuni, 2020, Alkali Mohammed Liman ya ce EFCC sun gaza gamsar da kotu cewa da kudin sata sanata Bukola Saraki ya saye gidajensa.

Mai shari’a Mohammed Liman ya ce babu hujjar da ta nuna cewa gwamnatin Kwara ce ta biya bashin da Bukola Saraki ya dauka daga wani banki domin maida kudin kadarorin.

Asali ma Alkalin ya tabbatar da cewa Bukola Saraki ya saye wadannan gidaje da ke Legas ne ta hanyar aron kudi da ya karba daga banki, don haka ya yi watsi da zargin hukumar.

A karshe Alkali kotun ya dakatar da shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Satumba. A wannan rana ne EFCC za ta kira shaidu domin warware tafka da warwarar da ta ke yi a gaban kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel